Dokar Zabe: Rikici Ta Barke a Zaman Majalisar Dattawa kan Wasu Kalaman Akpabio
- Sanatoci sun barke da hayaniya a zamansu na yau Talata yayin muhawara kan dokar tura sakamakon zabe ta intanet kai tsaye daga rumfunan zabe
- Rahoto ya nuna cewa an dan samu hatsaniyar ne bayan shugabam Majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanto wasu shawarwarin da aka gabatar
- Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan gyaran dokar zabe da Majalisar dattawa ta yi a makon jiya, inda ta kii amincewa da wajabta tura sakamako ta intanet
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rikici da hayaniya sun kaure a Majalisar dattawa yayin muhawara kan dokar tura sakamakon zabe ta intanet kai tsaye daga kowace rumfar zabe a Najeriya.
Rahoton da ya riske mu ya nuna cewa sanatoci sun barke da hayaniya da ka-ce-na-ce a tsakaninsu a zaman gaggawa da suka gudanar yau Talata, 10 ga watan Fabrairu, 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan
Dokar zabe: Amaechi ya tafi da dansa wajen zanga zanga a majalisar dattawa, ya fadi dalili

Source: Facebook
Dalilin zaman gaggawa a Majalisar dattawa
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar dattawa ta kira zaman gaggawa ne domin nazari da amincewa da rahoton ayyuka na zaman ranar 4 ga watan Fabrairu, 2026 wanda a cikinsa aka amince da kudurin Dokar Zabe.
Hakan na zuwa ne bayan takaddama da ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan shawarar da Majalisar ta yanke na fatali da sashen wajabta tura sakamakon zabe ta na’ura kai-tsaye.
Majalisar dattawan dai ta bar dokar tura sakamakon a yadda take tun 2022, ta ki yarda da bukatar wajabta tura sakamako ta intanet daga rumfunan zabe a cikin gyaran da ta yi wa Dokar Zabe.
Abin da ya haddasa hayaniya a Majalisa
Bayanai sun nuna cewa a zaman yau, hayaniya ta barke ne lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta shawarwarin da aka gabatar domin gyara ga Sashe na 60(3) na dokar zabe.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027
Sanata Akpabio ya karanta shawarwarin ne bayan da Sanata Tahir Monguno (APC, Borno) ya gabatar da kuduri a karkashin Dokar Majalisa (Order 1b 52(6)) cewa Majalisar ta janye matsayar da ta dauka a baya.
Wasu daga cikin sanatoci ba su gamsu da wasu daga kalmomi da aka yi amfani da su a cikin sabbabbin shawararin gyaran da Akpabio ya karanto ba, lamarin da ya tada hayaniya.

Source: Facebook
Sanata Enyinnaya Abaribe ya nemi a bi tsarin dokar majalisa don ba kowane sanata damar kada kuri'a shi kadai, yana mai dogaro da batun rabuwar kai a karkashin Dokar Majalisa ta 70.
Vanguard ta ce daga baya ya janye bukatar tasa, wanda hakan ka iya kawo cikas ga gyaran da ake son yi wa Sashe na 60(3), ma'ana bangaren da ya tanadi dokar tura sakamakon zabe ta intanet.
An yi zanga-zanga a Majalisa kan dokar zabe
A wani rahoton, kun ji cewa masu zanga-zanga sun taru a kofar Majalisar Tarayya domin neman a sanya dokar dora sakamakon zaɓe kai tsaye ta yanar gizo.
Wannan zanga-zangar tana zuwa ne sakamakon matsayar da Majalisar Dattawa ta ɗauka kan batun tura sakamakon zaɓe ta na'ura kai tsaye daga rumfunan zabe.
Tun farko dai Majalisar Dattawa ta ki yarda da kudurin wajabta tura sakamako kai-tsaye daga sabon gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2026 a makon da ya gabata.
Asali: Legit.ng