Wata Sabuwa: Bayan Turo Sojoji, An Hango Abin da Amurka Za Ta Yi a Zaben Najeriya na 2027

Wata Sabuwa: Bayan Turo Sojoji, An Hango Abin da Amurka Za Ta Yi a Zaben Najeriya na 2027

  • Tsohon kakakin Majalisar wakilai, Yakubu Dogaro ya yi hasashen abin da Amurka za ta yi a babban zaben 2027 a Najeriya
  • Dogara ya yi ikirarin cewa kasashe da dama a duniya ciki har da Amurka ba za su bari Najeriya ta rushe ba saboda illar hakan a nahiyar Afirka
  • Ya bukaci gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye ta tabbatar da martabarta a idon duniya domin gujewa matsaloli a nan gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Rt Hon Yakubu Dogara, ya bayyana cewa akwai yiwuwar Amurka ta taka rawar gani fiye da sa ido kadai a babban zaben Najeriya na 2027.

Rt. Hon. Dogara ya ce hakan na da nasaba da muradun kasar Amurka game da zaman lafiyar Najeriya da kuma tasirinta a nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

APC a Kano: An tsige mutumin Ganduje, 'yan bangaren Barau sun ware sun yi taro

Yakubu Dogara.
Tsohon shugaban Majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara Hoto: Yakubu Dogara
Source: Facebook

Dogara ya bayyana hakan ne a cikin shirin Inside Sources tare da Laolu Akande, wanda tashar Channels TV ke watsawa ranar Litinin.

Matsalar da aka samu a dokokin kasa da kasa

Ya yi gargadin cewa tsofaffin ka’idojin kasa da kasa sun raunana, wanda hakan ya bar kasashe, kowa na fafutukar kare muradunsa

"Tsarin duniya a yanzu ya ruguje. Gaskiyar magana ita ce muna a wani mataki wanda ko dai ka zama daya daga cikin masu cin abinci a teburi, ko kuma kai ne abincin da za a ci."

Dogara ya bayyana cewa dole ne Najeriya ta tashi tsaye cikin hikima wajen tabbatar da matsayinta a harkokin duniya, yana mai gargadin illar da za ta biyo baya idan kasar ta kasa daukar mataki da wuri.

A rahoton Guardian, tsohon dan Majalisar ya kara da cewa:

"Idan ba a yi hankali ba, idan ba mu yi abin da ya kamata ba, idan ba mu dauki dukkan matakan da suka dace na kasancewa a cikin tsari ba, ina ba ku tabbacin cewa za a iya yanke makomar Najeriya ba tare da mu ba."

Kara karanta wannan

2027: Magoya baya sun matsa, ana son Obi da Kwankwaso su hadu a kayar da Tinubu

Dogara ya hango shirin Amurka a Najeriya

'Dan siyasar ya kuma yi magana kan muhimmancin Najeriya ga Amurka da sauran kasashen duniya, inda ya lura cewa zaman lafiyar Najeriya na da tasiri mai girma fiye da iyakokinta.

"Abin damuwar shi ne, su [Amurka] ba za su taba barin Najeriya ta durkushe ba, domin idan Najeriya ta fadi, tasirin hakan zai iya sauya yadda nahiyar Afirka take a halin yanzu," in ji shi.
Shugaba Bola Tinubu da Trump.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: @OfficialABAT/X, @DonaldJTrump
Source: Twitter

A cewar Dogara, wannan gaskiyar ita ce ta sa manyan kasashen duniya suke sanya ido sosai kan yadda siyasar Najeriya da tafarkin dimokuradiyyarta ke tafiya, har da tsarin zabe.

Ya kara da cewa bisa bincikensa da kuma yanayin da yake gani, kulawar kasashen duniya ga Najeriya za ta kara tsananta yayin da babban zabe ke gabatowa.

An sake kai korafin Najeriya ga Amurka

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Mataimakin kakakin APC na Najeriya, Kwamred Timi Frank ya rubuta wasikar korafi zuwa ga shugaban Amurka, Donald Trump.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Tsohon dan majalisa ya shirya kara wa da Tinubu, zai nemi takara

Frank ya yi gargaɗin cewa dimokuradiyyar Najeriya na fuskantar barazana mai tsanani kuma tana iya fadawa cikin hargitsi idan ba a dakatar da shirye-shiryen maguɗin zaɓen 2027 ba.

Frank ya buƙaci Amurka da ta dauki mataki kan Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya zarga da jagorantar ƙoƙarin hana ’yan Najeriya damar zaɓar shugabannin da suke so.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262