Magana Ta Fito: El Rufai Ya Haska Abin da Ya Jawo Sabani tsakaninsa da Tinubu

Magana Ta Fito: El Rufai Ya Haska Abin da Ya Jawo Sabani tsakaninsa da Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya tabo batun sabanin da ke tsakaninsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Nasir El-Rufai ya bayyana cewa sabanin yadda mutane ke zato, ba shi da wata alaka ta abota da tsohon gwamnan na jihar Legas
  • El-Rufai ya bayyana cewa ko da ya zama Minista a karkashin gwamnati Tinubu, da sai ya yi murabus domin ba zai iya yin aiki tare da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fito fili ya bayyana dalilan dake tattare da takun-sakar da ke tsakaninsa da Shugaba Bola Tinubu.

Nasir El-Rufai ya nanata cewa sabanin nasu ya ginu ne kan ka'idojin gudanar da gwamnati, ba wai kiyayyar kashin kai ba.

El-Rufai ya yi magana kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: Kashim Shettima, Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Trust TV a ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Akpabio: El Rufa'i ya zargi Shugaban Majalisa da zama alaƙaƙai wajen gyara dokar zabe

Mece ce alakar Tinubu da El-Rufai?

El-Rufai ya fayyace cewa sabanin abin da jama'a ke zato, shi da Tinubu ba su taba samun kyakkyawar alaka ta kashin kai ba.

"Ban taba zama abokin Tinubu ba. Ba mu taba samun alaka ta kashin kai irin wadda nake da ita da Janar Buhari (marigayi) ba."

- Nasir El-Rufai

Me ya jawo sabanin Tinubu da El-Rufai?

El-Rufai ya bayyana cewa sabaninsa da gwamnatin Tinubu ya samo asali ne daga abin da ya kira bambancin ra'ayin gudanar da mulki.

"Ba wai mun yi fada da juna ba ne; kawai dai ba mu samu wuraren da ra'ayinmu ya zo daya ba. Ni ina shiga gwamnati ne domin na bauta wa jama'a kuma na samar da sakamako na kwarai, ba wai don na arzuta kaina ko na nada mukarrabai na ba,"
"Tsarin wannan gwamnati ya saba wa duk abin da aka koya mini a matsayina na Musulmi, dan Arewa, kuma dan Najeriya."

Kara karanta wannan

El Rufai ya yi fallasa, ya tona gaɓar da ake yin magudin zabe a Najeriya

"Sun zo ne domin su ci gajiyar gwamnati, su arzuta kansu. Mu mutane ne mabanbanta, muna tafiya ne a kan layuka biyu mabanbanta wadanda ba za su taba haduwa ba."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya ce ba zai iya aiki da Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Dalilin El-Rufai na hakura da mukamin Minista

Haka kuma, ya bayyana cewa shawarar da ya yanke na kin karbar mukamin minista daga hannun Shugaba Tinubu ta ginu ne a kan wadannan ka'idoji.

El-Rufai wanda aka tantance a majalisa a karo na biyu a 2023 ya kara da cewa da Tinubu ya nada shi a matsayin minista, a karshe dole zai ajiye aikin.

"Da na karbi mukamin Ministan da aka ba ni a bainar jama'a, to da na yi murabus. Manufofinmu na yadda ake gudanar da gwamnati sun bambanta nesa ba kusa ba."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya goyi bayan gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya goyi bayan matsayar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dauka kan yaki da 'yan bindiga.

Nasir El-Rufa'i ya goyi bayan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na kin biyan kudin fansa ga 'yan bindigan da ke garkuwa da mutane.

Tsohon gwamnan ya ce ya kamata a karfafa wa gwamnati gwiwa a kan wannan mataki, domin hakan zai taimaka wa Najeriya wajen yaki da tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng