Akpabio: El Rufa'i Ya Zargi Shugaban Majalisa da Zama Alaƙaƙai wajen Gyara Dokar Zabe
- Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da jawo matsala a dokar zabe
- El-Rufai ya ce ba Majalisar Dattawa ba ce matsala, illa shugabancin Akpabio da ya hana ruwa gudu wajen tabbatar da abin da ake bukata
- Ya bukaci sanatoci masu adawa da kudirin su hada kai su fito fili su dakile jagorancin da Akpabio ke yi, da a ganinsa yana jawo nakasu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya caccaki tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Malam Nasir El-Rufai wanda ya yi shekaru takwas a mulkin Kaduna ya zargi Akapbio da zama babban cikas a yunkurin gyara Dokar Zabe a Najeriya.

Source: Twitter
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da Trust TV da NG Affairs ta wallafa a shafin X, inda ya bayyana cewa ba dukkanin Sanatocin ne ke hana ruwa gudu game da dokar.
El-Rufa'i ya soki Shugaban majalisa, Akpabio
Daily post ta wallafa cewa El-Rufa'i ya bayyana cewa matsalar da ake samu a kan dokar zabe ba ta Majalisa ba ce, illa mutum guda da ke jagorantarta.
A kalamansa:
“Ba Majalisar Dattawa ba ce matsalar a nan. Akpabio ne matsalar..."
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa irin salon shugabancin Akpabio ne ke haddasa rudani da rashin amincewa a tsakanin ‘yan kasa game da kudirin da ake kokarin gabatarwa.
Ya kara da bayyana cewa ana amfani da Majalisar Dattawa ne wajen biyan bukatun wasu manyan ‘yan siyasa.
Manya Akpabio yake yi wa aiki - El-Rufa'i
El-Rufai ya kuma zargi Shugaban Majalisar Dattawa da zama kamar mai biyayya kawai ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya kara da zargin cewa Akpabio ba ya aiki da kansa, sai dai bisa umarnin wasu masu karfin fada a ji a siyasa.

Source: Facebook
Ya yi kira ga sanatocin da ba su goyi bayan gyaran Dokar Zaben ba da su hada kai su fito fili su nuna adawarsu lokacin da Majalisar Tarayya ta koma zama.
El-Rufa'i ya ce:
“Dole ne sanatocin su hada kai, su yi zanga-zanga, su hana hakan faruwa."
Ya kara da bayyana cewa wannan yunkuri da Akpabio ke ci gaba da yi ya hana a tabbatar da okar zabe da za a aminta da ita babbar illa ce ga kasar nan.
Malam El-Rufa'i ya magantu kan zaben 2027
A baya, kun ji cewa Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa jam’iyyar hadaka ba za ta yi amfani da tsarin karba-karba wajen fitar da dan takarar shugaban kasa ba.
El-Rufai ya jaddada cewa duk wanda ke da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwar ADC zai samu cikakkiyar dama, ba tare da takura ko fifita wani yanki ba.
A cewarsa, jam’iyyar ta kuduri aniyar gina tafiyarta a kan adalci da gaskiya a tsarin siyasa, domin jawo hankalin ‘yan Najeriya da ke neman sauyi na gaskiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

