APC a Kano: An Tsige Mutumin Ganduje, 'Yan Bangaren Barau Sun Ware Sun Yi Taro
- Rikicin cikin jam’iyyar APC a Kano ya kara tsananta bayan sabani tsakanin bangaren Barau Jibrin da na tsohon gwamna Abdullahi Ganduje kan jagoranci
- An ce an tsige wani jagoran jam’iyya a birnin Kano da ke da alaka da Ganduje, lamarin da ya jawo tarukan masu ruwa da tsaki guda biyu a wurare daban-daban
- Sabani kan tsarin sulhu da hanyar tattaunawa ya nuna yadda rarrabuwar kai ke kara zurfi a cikin jam’iyyar bayan sauya shekar gwamna Abba Kabir Yusuf
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano, Najeriya – Jam’iyyar APC a Jihar Kano na fuskantar sabon babin rikicin cikin gida bayan sabani tsakanin bangarorin da ke biyayya ga Barau Jibrin da kuma Abdullahi Ganduje.
Lamarin ya kunno kai ne a karamar hukumar birni, inda ake ganin yankin na da matukar muhimmanci ta fuskar yawan masu kada kuri’a.

Source: Facebook
Tashar Arise News ta ce rikicin ya kara bayyana ne bayan taron masu ruwa da tsaki da aka shirya domin hada kai ya rikide zuwa taruka biyu daban-daban, alamar cewa sabanin ya zurfafa fiye da yadda ake zato.
An tsige na kusa da Abdullahi Ganduje
Rahotanni sun bayyana cewa an tsige Muntari Ishaq, wani jagoran APC da ke da goyon bayan Ganduje a birni, bayan taron masu ruwa da tsaki da aka ce ya hada wakilai daga mazabu 13 na karamar hukumar.
A cewar bayanan da suka fito, mahalarta taron sun cimma matsaya daya na korar Ishaq daga jam’iyyar, matakin da ya kara rura wutar rikici tsakanin bangarorin biyu.
Asalin manufar taron, a cewar wasu jiga-jigan jam’iyyar, ita ce karfafa hadin kai da lalubo hanyar sulhu tsakanin bangaren Ganduje da na Barau, amma hakan bai samu ba.
Jam'iyyar APC ta yi taruka 2 a Kano
Bayan kasa cimma matsaya kan dandalin tattaunawa guda daya, bangarorin biyu sun gudanar da taruka a wurare daban-daban, abin da ya kara nuna rarrabuwar kai.
Bangaren Ganduje ya gana da shugabanni da suka hada da Shugaban APC na Kano Municipal, Alhaji Sani Abubakar Mai Fata Sharada, Muntari Ishaq Yakasai, Baffa Babba Dan’agundi, Sagir Koki.
Sauran sun hada da Hon. Salim Hashim Gwangwazo, Nura Hussain, Hon. Nabil Sarki Daneji, Hon. Ibrahim Kankarofi da Hon. Kabiru Labour.

Source: Facebook
A daya bangaren kuma, magoya bayan Barau Jibrin sun gudanar da nasu taron a Sultanate Suite karkashin jagorancin Hon. Salisu Maje Ahmed Gwangwazo.
Sauran sun hada da Malam Ibrahim Kankarofi, Hon. Fa’izu Alfindiki, Hon. Dan Bello, Alhaji Hamza Darma da Barrista Faruk Iya Sambo.
Wane ne Muntari Ishaq a APC?
Legit Hausa ta fahimci Muntari Ishaq Yakasai yana cikin wadanda ake ganin za su nemi kujerar shugaban jam'iyyar APC na reshen Kano a zaben da za a yi kwanan nan.
Tsohon 'dan siyasar ya nemi kujerar majalisar wakilan tarayya a zaben 2023 domin ya canji Sha'aban Sharada, sai dai Sagir Koki da NNPP ne suka yi nasara a birni.
A gwamnatin Ganduje, Yakasai ya rike mukamin kwamishina na ayyuka na musamman kuma da shi aka yi a mulki tun wa'adin farko na Rabiu Musa Kwankwaso a Kano.
Sharhin bangaren Kwankwasiyya a Kano
Yayin da yake sharhi kan abin da ya faru, hadimin Sanata Rabiu Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
“Mu a Kano Municipal taron masu ruwa da tsaki na APC guda biyu aka yi, kowane bangare sun yi nasu gudun kada a tashi baram-baram.
"Wanda ya ce ya fita daga NNPP saboda rikicin cikin gida, sai ga shi ya zo inda ake taron masu ruwa da tsaki guda biyu saboda wannan bangaren baya shiri da dayan bangaren, kowa ya yi nasa.”
Kwankwaso ya yi taro a Dubai
A wani labarin, mun kawo muku cewa jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da wasu 'yan jihar Kano mazauna Dubai.
'Yan Kwankwasiyya mazauna Dubai sun jaddada biyayya da Rabiu Musa Kwankwaso bayan Abba Kabir ya koma jam'iyyar APC mai mulki.
Kwankwaso ya bayyana musu cewa babun dalilin ja da baya a harkar Kwankwasiyya saboda wasu da ake tafiya sun yi abin da ya kira butulci.
Asali: Legit.ng


