Sanata Ya Gama Nazari, Ya Fito Takarar Gwamna a Inuwar APC a Zaben 2027
- Sanatan Kwara ta Kudu, Lola Ashiru ya bayyana shirinsa na neman takarar gwamnan jihar a babban zaben 2027 da ke tafe
- Mataimakin shugaban masu rinjaye a Majalisar dattawan ya ce ya yanke shawarar neman zama gwamnan Kwara ne bayan dogon nazari
- 'Dan Majalisar dattawan ya yi fatali da batun karba-karba da shiyyar Kwara ta Arewa ke fafutuka, ya ce a bar kowa ya gwada sa'arsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara, Nigeria - Mataimakin shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Lola Ashiru, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kwara a babban zaɓen 2027.
Ashiru, sanata mai wakiltar mazaɓar Kwara ta Kudu, ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin mambobin ƙungiyar ’yan jarida (NUJ) reshen jihar Kwara, a gidansa da ke garin Offa.

Source: Facebook
Sanata ya fito takarar gwamna a Kwara

Kara karanta wannan
Tun kafin a yi nisa, an sauke gwamna daga matsayin shugaban kwamitin taron APC na kasa
A rahoton da Premium Times ta hada, sanatan ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne saboda zai iya kawo ci gaba ga jihar Kwara.
"Zan tsaya takara ne saboda na yi imanin cewa ina da kyakkyawar niyya kuma ina da cancantar da zan iya mulkin jihar Kwara na tsawon shekaru huɗu masu zuwa, tun daga 2027.
"Ina jin na fi kowa fahimtar mutanen jihar nan da kuma ita kanta jihar Kwara, domin na daɗe a cikinta fiye da kowane mai neman takara," in ji shi.
Batun karba-karba a jihar Kwara
Gwamna mai ci yanzu, AbdulRahman AbdulRazaq, ya fito ne daga mazaɓar Kwara ta Tsakiya, yayin da wanda ya gada, Abdulfatah Ahmed ya fito daga Kwara ta Kudu.
A nata ɓangaren, mazaɓar Kwara ta Arewa ba ta taɓa samar da gwamna ba tun bayan Shaaba Lafiagi, wanda ya yi mulki na tsawon watanni 22 kacal daga Janairu 1983 zuwa Nuwamba 1985.
Wannan ya sa ake ta fafutukar cewa kamata ya yi a ba wa Kwara ta Arewa takarar gwamnan a 2027. Sai dai Mista Ashiru ya jaddada cewa ya kamata a zaɓi gwamna ne bisa cancanta.
"Abin da ya fi kyau shi ne a ba kowa dama ya zaɓi shugaban da ya fi dacewa. Ina tausayawa Kwara ta Arewa domin an daɗe ba a ba su mulki ba; suna da kyakkyawan dalilin cewa lokacinsu ne, amma ba haka abin yake ba."

Source: Facebook
Yadda za a magance matsalar tsaron Kwara
Da yake magana kan harin da ’yan ta'adda suka kai a ƙaramar hukumar Kaiama makon jiya, ɗan majalisar ya yi kira ga gwamnati a kowane mataki da ta ƙarfafa tsaron iyakoki ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa ga mazauna yankunan.
A ruwayr Punchi, sanatan ya ce:
"Ina jin dole ne mu kula da hanyoyin da suka haɗa mu da maƙwabtanmu. Matakin farko kuma mafi mahimmanci shi ne yaɗa arziki da ci gaba a waɗannan yankuna.
Gwamnan Kwara ya ce APC kadai mafita
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa APC ita ce jam’iyya mafi dacewa da mulkin Najeriya.
Shugaban kungiyar NGF ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da taron masu ruwa da tsaki na APC a jihar Kwara, tare da fara rajistar yanar gizo da tantance mambobin jam’iyyar.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa duk masu niyyar tsayawa takarar kujerun siyasa a 2027 za su samu dama iri daya, ba tare da nuna wariya ba.
Asali: Legit.ng
