Akwai Matsala: An Sake Kai Korafin Najeriya ga Shugaban Amurka, Donald Trump
- Tsohon mataimakin kakakin APC na kasa, Timi Frank ya rubuta wasikar korafi zuwa ga shugaban Amurka, Donald Trump
- A wasikar, Frank ya bukaci Shugaba Trump ya gaggauta daukar mataki domin ceto tsarin dimokuradiyyar Najeriya
- Daga cikin abubuwan da ya rubuta a wasikar akwai koke kan gyaran dokar zaben Najeriya, wanda ya tayar da kura a kasar nan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC ta ƙasa, Kwamared Timi Frank, ya aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump, takardar koke.
Frank ya yi gargaɗin cewa dimokuradiyyar Najeriya na fuskantar barazana mai tsanani kuma tana iya fadawa cikin hargitsi idan ba a dakatar da shirye-shiryen maguɗin zaɓen 2027 ba.

Source: Facebook
Hakan na kunshe a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai kwanan wata 7 ga Fabrairu, 2026, da Timi Frank ya tura zuwa ga Shugaba Trump, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Timi Frank ya kai wa Shugaba Trump korafi
Ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ƙoƙarin kawo tsarin mulki na jam’iyya ɗaya, matakin da ya bayyana a matsayin “kisan kiyashin siyasa” ga ’yan Najeriya.
Ya yi kira ga Trump da ƙasashen duniya da su sa baki cikin gaggawa, yana mai gargaɗin cewa rashin ɗaukar mataki na iya kaiwa ga tarzoma, rikici da kuma rugujewar doka da oda kafin 2027.
“Babban zaɓen Najeriya da aka tsara gudanarwa a watan Fabrairun 2027 yana fuskantar barazana mai girma. Idan ba a magance abubuwan da ke faruwa yanzu ba, suna iya haifar da hargitsi da rashin bin doka,” in ji Frank.
Abin da Timi Frank yake zargi
Frank ya yi zargin cewa Majalisar Dattawa na yi wa dokar zaɓe zagon ƙasa, inda ya zargi sanatoci da cire wasu muhimman sassa na Dokar Zaɓe ta 2022 da mafi yawan Najeriya suka amince da su.
Ya kara da cewa:
“Jam’iyya mai mulki, tare da haɗin gwiwar Majalisar Dattawa ƙarƙashin Shugaban Majalisar da ake zargi da son zuciya, sun fara shimfiɗa dabarun tafka maguɗi a zaɓen 2027.”
Tsohon kakakin na APC ya kuma soki sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya yi nuni da ƙarancin masu jefa ƙuri’a da rahotannin masu sa ido wanda ya nuna rashin sahihancin zaɓen.
Matakin da ake so Amurka ta dauka
Frank ya buƙaci Amurka da ta dauki mataki kan Shugaban Majalisar Dattawa, wanda ya zarga da jagorantar ƙoƙarin hana ’yan Najeriya damar zaɓar shugabannin da suke so., cewar rahoton Daily Post.
Haka zalika, ya yi zargin cewa ana matsa wa hukumomin tsaro kamar sojoji, ’yan sanda, da kuma fannin shari’a lamba don su zama ’yan amshin shatar jam’iyya mai mulki.

Source: Getty Images
Ya kammala wasiƙar tasa da rokon Trump da ya kasance mai taka-tsantsan wajen mu’amala da gwamnatin Najeriya, domin gujewa halatta abin da ya kira "zalunci da danne haƙƙin jama’a."
An an taso Sanata Akpabio a gaba
A wani labarin, kun ji cewa jigo a jam'iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, ya soki Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio kan gyaran dokar zaben Najeriya.
Okonkwo ya nuna damuwarsa kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan amincewar da Majalisar dattawa ta yi da kudirin gyaran dokar zabe ta 2026.
Ya ce dokar zaben da Akpabio ya jagoranci amincewa da ita a Majalisar dattawa ta cancanci a tsige shi daga mukaminsa idan ya ki yin murabus.
Asali: Legit.ng


