Jam'iyyar NNPP Ta Kara Daukar Zafi, Ta Nesanta Kanta daga Kalaman Kwankwaso
- Kalaman da jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso ya yi cewa ya dauki Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa wurin alkalan kotun koli sun tada kura
- Tsagin jam'iyyar NNPP da Agbo Major ke jagoranta ya nesanta kansa da maganar da Kwankwaso ya yi, ya ce lokacin ba dan jam'iyyarsu ba ne
- Wannan na zuwa ne bayan kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta kai korafin Sanata Kwankwaso gaban Sufetan Yan Sandan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - NNPP ta nesanta kanta da kalaman tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, cewa ya kai Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen wasu alkalan Kotun Koli a 2019.
Tsagin NNPP karkashin jagorancun Dr. gbo Major ya jaddada cewa Kwankwaso ba dan jam'iyyar ba ne a shekarar 2019 lokacin da ake zargin wannan lamari ya faru.

Source: Facebook
Hakan dai na kunshi ne a cikin wata sanarwa da Sakataren NNPP na Ƙasa, Kwamared Oginni Olaposi Sunday, ya sanya wa hannu, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Tsagin NNPP ya aika sako ga kungiyar NBA
Jam’iyyar ta buƙaci ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) da ta goge sunan NNPP daga kowace irin takardar ƙorafe-ƙorafe da ta miƙa wa Sufeto Janar na ƴan sanda kan wannan magana.
"Bari mu fayyace gaskiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba mamban NNPP ba ne a 2019 lokacin da ake zargin ya kai Gwamna Abba Kabir Yusuf ganin wasu alkalan Kotun Koli,” in ji Oginni.
Sanarwar ta bayyana cewa Kwankwaso ya shiga jam’iyyar NNPP ne kawai ’yan watanni kafin zaɓen 2023, tare da mutane irin su Buba Galadima, Sanata Suleiman Hunkuyi, da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Haka kuma, jam’iyyar ta musanta rahotannin da ke cewa Kwankwaso na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ta.
Sanarwar ta kara da cewa halastaccen wanda ya kafa NNPP shi ne Dr. Boniface Okechukwu Aniebonam.

Kara karanta wannan
Kalaman Kwankwaso na taimaka wa Abba Kabir a shari'ar 2019 sun jefa shi a matsala
Jam'iyyar NNPP ta zargi da Kwankwaso
NNPP ta kuma zargi Kwankwaso da ƙoƙarin ƙwace jam’iyyar bayan ya shiga, inda ta ce ya canza tambarin jam’iyyar da launukanta zuwa na ƙungiyarsa ta Kwankwasiyya ba tare da amincewar uban jam'iyya ko kwamitin amintattu (BoT) ba.
"Abin bakin ciki ne yadda Sanata Kwankwaso ya yi ƙoƙarin mayar da ikon mallakar wanda ya kafa NNPP zuwa amfanin kansa,” in ji Sunday.
Olaposi Sunday ya tunatar da jama’a cewa tuni aka riga aka kori Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Source: Facebook
Ya kara da cewa kotu ta yi watsi da karar da tsagin Kwankwaso ya kalubalanci jagorancin Dr. Agbo Major (Shugaban NNPP na Ƙasa) da Oginni Olaposi Sunday (Sakatare).
NBA za ta kai korafi kan Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta amince cewa za ta rubuta koke ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya kan kalaman Rabi'u Musa Kwankwaso.
Kungiyar ta ce za ta tura korafin ne ga 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro kan zargin tsoma baki a shari’ar zaben Kano a 2019.
Lauyoyin sun ce irin wadannan kalamai, ko gaskiya ne ko a’a, na da hatsari ga amincewar jama’a kan ‘yancin kai da sahihancin bangaren shari’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

