Rikicin PDP: Bangaren Turaki Ya Yi Bambami bayan INEC Ta Watsa Musu Kasa a Ido

Rikicin PDP: Bangaren Turaki Ya Yi Bambami bayan INEC Ta Watsa Musu Kasa a Ido

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya na ci gaba da samun kanta cikin rikici wanda y. Ki ci ya ki cinyewa na lokaci mai tsawo
  • Hukumar zabe ta INEC ta gayyaci kwamitin rikon kwarya na PDP da Nyesom Wike ke marawa baya zuwa wajen taron jam'iyyun siyasa
  • Wannan mataki ya harzuka bangaren PDP da Kabiru Tanimu Turaki SAN ke jagoranta, inda suka yi martani mai zafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kwamitin zartarwa na kasa (NWC) ta jam’iyyar PDP da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta, ta soki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Bangaren na Turaki ya yi sukar ne bisa amincewa da kwamitin rikon kwarya da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ke mara wa baya.

Bangaren Turaki na PDP ya soki hukumar INEC
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan da Shugaban tsagin PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki Hoto: INEC NIGERIA, Kabiru Tanimu Turaki, SAN
Source: Facebook

Sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP na kasa, Ini Ememobong ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanya a shafin X a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

INEC ta dauki bangare 1 a rikicin PDP, ta yi zama da shugabannin jam'iyyu a Abuja

Kotu ta yi hukunci a rikicin jam'iyyar PDP

A ranar Juma’ar da ta gabata, babbar kotun tarayya da ke Ibadan ta soke babban taron PDP na kasa da aka gudanar a ranar 15 ga Nuwamba, 2025, a Ibadan, jihar Oyo.

Kotun ta umarci Kabiru Tanimu Turaki (SAN) da sauran wadanda aka zaba a wajen taron da su daina bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar na ƙasa.

Wane martani bangaren Turaki ya yi wa INEC?

Bangaren na Turaki ya bayyana matakin a matsayin wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma mai tayar da hankali.

Hakazalika ya gargaɗi INEC cewa zai bi dukkan hanyoyin doka da ake da su domin ƙalubalantar matakin da hukumar ta dauka.

Ememobong ya bukaci mambobin jam’iyyar da su zauna lafiya cikin haƙuri, yayin da ake jiran hukuncin kotuna kan rikicin shugabancin jam’iyyar da ke gudana.

"Mun samu labarin cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gayyaci shugabannin jam’iyyun siyasa zuwa taro a yau, inda ta aika gayyata ga wasu tsofaffin mambobin jam’iyyarmu da ke ikirarin jagorantar wani abin da suka kira kwamitin rikon kwarya na kasa, domin su wakilci jam’iyyarmu, alhali babu wani tanadi makamancin haka a kundin tsarin mulkinmu.”

Kara karanta wannan

Wike ya shiga tsilla tsilla, APC ta fadi matsayinsa wurinta kan rigima da Fubara

"Wannan mataki, duk da cewa yana da tayar da hankali kuma na iya haifar da tarzoma, za mu fuskance shi ta dukkan hanyoyin doka da suka dace."
"Ko da yake ba abin mamaki ba ne daga wannan shugabancin INEC na yanzu, ana sa ran hukuma mai zaman kanta za ta lura da cewa batutuwan suna gaban kotun daukaka kara (ciki har da hukuncin da suke dogara da shi), wanda idan aka yanke, zai shafi batun da ake magana a kai."
"Muna tabbatar da cewa INEC ba za ta zaɓi shugabanni ga jam’iyyarmu ba.”
"Saboda haka, muna kira ga dukkan mambobin jam’iyyarmu da su kasance cikin natsuwa, domin nan ba da jimawa ba kotun daukaka kara za ta saurari tare da yanke hukunci kan dukkan shari’o’in da suka shafi shugabancin jam’iyyarmu.”

- Ini Ememobong

Hukumar INEC ta harzuka bangaren Kabiru Tanimu Turaki na PDP
Shugaban PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki a ofis Hoto: Kabiru Tanimu Turaki, SAN
Source: Instagram

Sanatocin PDP sun sauya sheka zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta sake samun koma baya bayan wasu daga cikin sanatocinta daga jihar Taraba sun sauya sheka zuwa APC.

Sanata Haruna Manu (Taraba ta Tsakiya) da Sanata Shuaibu Isa Lau (Taraba ta Arewa) sun aike da wasiƙun murabus ɗinsu ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Sanata Shuaibu Isa Lau ya bayyana cewa manufofin jam'iyyar APC sun yi daidai da burinsa na yi wa al'ummar Taraba ta Arewa hidima yadda ya kamata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng