INEC Ta Dauki Bangare 1 a Rikicin PDP, Ta Yi Zama da Shugabannin Jam'iyyu a Abuja
- Hukumar INEC ta yi zama da shugabannin jam'iyyun siyasa a babban ofishinta na kasa da ke Abuja yau Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026
- A taron, an ga wakilan tsagin PDP karkashin jagorancin Abdulraham Mohammed, wanda ke samun goyon baya daga Ministan Abuja, Nyesom Wike
- Hakan na zuwa ne bayan shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya jaddada cewa hukumar za ta yi biyayya ga hukuncin kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Alamu sun nuna cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta karbi hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke kwanan nan kan rikicin shigabancin PDP.
Hukumar INEC ta gayyaci tsagin PDP ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Mohammed da Sanata Samuel Anyanwu zuwa taron jam’iyyun siyasa da aka shirya domin tattaunawa kan babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Wakilan tsagin Wike sun halarci taron INEC
Jaridar Leadership ta tattaro cewa wannan tsagi yana samun goyon baya daga Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), a rigingimun da suka ki karewa a cikin jam'iyyar PDP.
Tsagin Wike ne suka wakilci jam’iyyar PDP da ke fama da rikici a wurin taron masu ruwa da tsaki da hukumar zaɓen ta gudanar yau Alhamis, 5 ga watan Fabrairu, 2026.
Idan za a iya tunawa, kwanan nan ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Ibadan, Jihar Oyo, ta soke tsagin jam'iyyar PDP da Barista Tanimu Turaki ke jagoranta.
Tsagin Tanimu Turaki na samun goyon baya daga gwamnonin PDP kamar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
INEC ta amince da tsagin a Nenadi a LP
Haka kuma, an hango kwamitin riƙo na jam’iyyar LP ƙarƙashin jagorancin Sanata Nenadi Usman a wurin taron.

Kara karanta wannan
Kalaman Kwankwaso na taimaka wa Abba Kabir a shari'ar 2019 sun jefa shi a matsala
Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da, shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yelwatda, wakilan jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark da sauran shugabannin jam’iyyu daban-daban.
Matsayar INEC kan shari’un kotu
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa INEC ta yanke shawarar yin biyayya ga hukuncin kotun da ta amince da shugabancin Sanata Nenadi Usman a jam’iyyar LP.
Farfesa Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron masu ruwa da tsaki na kafafen yada labarai, wanda ya gudana a Abuja.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa, a ko yaushe INEC a shirye take ta bi duk wani hukuncin kotu na gaba wanda zai iya soke hukuncin da ake kai yanzu, kamar yadda The Nation ta rahoto
Wannan mataki na INEC ya nuna cewa hukumar tana bin umarnin kotu ne wajen mu’amala da jam’iyyun da ke fama da rikicin shugabanci yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Hukumar INEC ta yi wa jam'iyyu 2 rijista
A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar INEC ta amince da bukatar wasu kungiyoyi masu neman yin rajista a matsayin jam'iyyun siyasa.

Kara karanta wannan
Ana batun dokar zabe, INEC ta yi wa sababbin jam'iyyu rajista daga cikin 171 da suka nema
Hukumar INEC ta yi rajista ga sababbin jam’iyyun siyasa guda biyu daga cikin wadanda suka nemi bukatar hakan a wajenta.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya sanar da cewa sababbin jam’iyyun da aka yi wa rajista su ne DLA da NDC.
Asali: Legit.ng
