'APC Ta Tsorata, Ta Fara Shirin Magudi a Zaben 2027,' ADC

'APC Ta Tsorata, Ta Fara Shirin Magudi a Zaben 2027,' ADC

  • Jam’iyyar ADC ta ce Majalisar Dattawan da APC ke jagoranta na ƙoƙarin lalata sahihancin zaɓen 2027 ta hanyar ƙin amincewa da tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo
  • Jam’iyyar ta bayyana matakin Majalisar a matsayin koma-baya, tana mai cewa hakan na nuni da tsoron APC na fuskantar sahihin zaɓe duk da rinjayen siyasar da take da shi
  • ADC ta yi kira ga Kwamitin Haɗaka kan Dokar Zaɓe da ya yi watsi da shawarwarin Majalisar Dattawa tare da amincewa da gyare-gyaren da za su kare dimokuraɗiyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta zargi APC da ke mulki da shirya hanyoyin tafka maguɗin zaɓen 2027 ta hanyar sauya muhimman tanade-tanaden Dokar Zaɓe.

Jam’iyyar adawar ta bayyana hakan ne bayan Majalisar Dattawa ta 10 da APC ke da rinjaye a cikinta, ta ƙi amincewa da tanadin tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Lauya ya roki kotun Kano, ta saukaka wa Shehin Darika da aka rufe a kurkuku

Bola Ahmed Tinubu, Godswill Akpabio da Bolaji Abdullahi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hagu, Godswill Akpabio a tsakiya da Bolaji Abdullahi a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Barau I Jibrin|Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ya wallafa a X cewa wannan matakin koma-baya ne ga tsarin dimokuraɗiyya, kuma yana nuni da yunƙurin murɗe sakamakon zaɓe tun kafin a kai ga 2027.

Zargin jam'iyyar ADC ga majalisar dattawa

Jam'iyyar ADC ta bayyana takaicinta kan yadda Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da muhimman gyare-gyare da za su inganta sahihanci da gaskiyar zaɓe a Najeriya.

Ta ce kin amincewa da tura sakamakon zaɓe ta lantarki wata dabara ce da ke da nufin tauye ikon ‘yan ƙasa da kuma lalata amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.

Sukar da ADC ke yi wa APC

Baya ga batun tura sakamakon zaɓe, ADC ta ce Majalisar Dattawa ta kuma yanke shawarar rage wa’adin sanar da gudanar da zaɓe da kuma rage lokacin wallafa jerin ‘yan takara daga kwanaki 150 zuwa 60.

A cewar jam’iyyar, waɗannan gyare-gyare za su jefa INEC cikin matsanancin ƙalubale na aiki, tare da buɗe ƙofofi ga cin zarafi da rikice-rikice a zaɓuka masu zuwa.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Majalisa ta cimma matsaya kan tura sakamako ta yanar gizo

Sanarwar ta ce an tsara waɗannan tanade-tanadene ne domin samar da kariya daga maguɗi da kuma dawo da amincewar masu zaɓe, amma APC ta yi amfani da rinjayenta a Majalisar don sauya dokokin domin moriyarta.

Zargin tsoron sahihin zaɓe a 2027

ADC ta bayyana cewa matakan da APC ke ɗauka na nuna tsoron fuskantar sahihin zaɓe, musamman ganin halin ƙunci da wahala da jama’a ke ciki a halin yanzu.

Jam’iyyar ta ce babu wanda ya yi tsammanin APC za ta kai wannan mataki na kin amincewa da gyara Dokar Zaɓe domin neman mulki ta kowace hanya.

Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

ADC ta yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su ƙi amincewa da matakin Majalisar Dattawa, tana mai cewa hakan na raunana dimokuraɗiyya.

Haka kuma, jam’iyyar ta buƙaci Kwamitin Haɗaka kan Dokar Zaɓe da ya yi watsi da shawarwarin Majalisar Dattawa, tare da amincewa da gyare-gyaren da za su dace da ƙa’idojin dimokuraɗiyya da muradin al’ummar Najeriya.

2027: Pantami ya sabunta katin APC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya sabunta katin zama dan jam'iyyar APC a Gombe.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta rufe bakin masu surutu, ta yi gyara a dokar zaben Najeriya

Tsohon ministan ya bayyana cewa mutane da dama suna kallon kamar yanzu ya fara siyasa amma tun kafin kafa APC ya ke harkar.

Sheikh Pantami ya ce tun 2001 suke zuwa wajen marigayi Muhammadu Buhari domin kokarin shawo kan shi ya shiga harkokin siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng