Yadda Sheikh Pantami Ya Ki Amsa wa Tinubu da Aka Yi Masa Tayin Mukaman Gwamnati
- Farfesa Isa Ali Pantami ya sabunta rajistar zama dan jam'iyyar APC a Gombe inda ya bayyana gaskiyar alakarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Malamin ya bayyana cewa har yanzu yana ba Tinubu shawarwari kuma yana karba saboda kokarinsa a nasarar shugaban kasar a zaben 2023
- Pantami ya kuma fadi dalilin da ya sa bai karbi tayin mukamai uku da Tinubu ya yi masa ba, yayin da ake zargin zai nemi takarar gwamna a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali, ya sabunta rajitar zama ɗan jam'iyyar APC a mazaɓar Pantami dake cikin birnin Gombe.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa malamin yana shirin komawa jam'iyyar ADC domin takarar gwamnan Gombe a zaɓen 2027.

Source: Twitter
A wani bidiyo da Leadership Hausa ta wallafa a shafinta na X, Pantami ya jaddada cewa har yanzu yana nan daram a cikin jam'iyyar APC, kuma yana da kyakkyawar dangantaka da Shugaba Bola Tinubu.
Alakar Pantami da shugaba Tinubu
A yayin jawabi ga jami'an jam'iyya, Pantami ya bayyana cewa mutane da dama ba su san irin rawar da ya taka ba wajen nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2023.
Ya bayyana cewa yana cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na ƙasa a matsayin babban mai ba da shawara na musamman, kuma shugaban kasar ne da kansa ya sanya hannu kan takardar naɗinsa.
A ofishin jam'iyyar APC, yayin sabunta rajistar APC, Farfesa Isa Pantami ya ce kujerarsa a kwamitin yakin neman zabe ta zarce ta darektocin kamfen APC a 2023.
Pantami ya ce:
"Kafuwar APC da mu aka yi ta ba wai mun shigo cikinta ba ne. Shugaba Bola Tinubu, mutane ba su sani ba ne, amma ina cikin kwamitin yakin neman zabensa.
"Matsayin da nake da shi a matakin kasa na yakin neman zabensa ya fi darakta, kuma shi da hannunsa ya sanya hannu kan takardar nada ni mai ba shi shawara a yakin neman zabensa a matakin kasa.
Tinubu ya yi wa Pantami tayin mukamai
Tsohon ministan ya kuma jaddada cewa har zuwa wannan lokaci ya na magana da Tinubu, kuma ya na ba shi shawarwari yana dauka idan bukatar hakan ta taso.
"Yau idan ina da wata shawara a gwamnati, da kansa zai turo in rubuta shawarar a takarda a kai masa. Maganata ta karshe da shi, shi ne ya kira ni da kansa muka gaisa. Saboda me? Ina da dabi'ar idan mutum yana shugabanci, ba na takura masa"
- Sheikh Isa Pantami.

Source: Twitter
Malamin ya ce Tinubu ya yi masa tayin mukamai har guda uku, amma ya ki karba, ya sanar da shi cewa zai mayar da hankali ne kan wasu abubuwa da ya sanya a gabansa.
"Zan yi adalci ga shugaban kasa, walLahi, ya ba ni matsayi daya, biyu, uku, ya ce in zaba, ya ce in zaba, na ce ranka ya radade na fi sha'awar in mayar da hankali kan abin da na sanya a gaba na. Don haka ni bai hana ni mukami ba.
- Sheikh Isa Pantami.
Kalli bidiyon jawabin Pantami a nan kasa:
Sakataren tsare-tsaren APC ya soki Pantami
A wani labari, mun ruwaito cewa, Sakataren tsare-tsaren APC a Gombe ya soki Sheikh Isa Ali Pantami a fili kan rashin ziyartar ofishin jam’iyya duk da mukamin da ya rike.
A cikin bidiyon da ya bazu a shafukan sada zumunta, sakataren ya nuna cewa duk masu yabon Pantami karya suke yi, kowa haushinsa yake ji, kawai an ki a fada masa ne.
Yayin da 'yan Najeriya suka yi martani kan kalaman sakataren, Sheikh Pantami ya kare kansa, ya bayyana cewa shi dan siyasar boye ne kuma ya dade a jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


