Pantami Ya Sabunta Rajistar Zama dan APC, Ya Tuna Shawarar da Buhari Ya Ba Shi kan Siyasar Gombe
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ziyarci sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Gombe domin sabunta rajistarsa ta zama mamba
- Tsohon Ministan na sadarwa a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya dade yana shiga cikin harkokin siyasa
- Farfesa Pantami ya kuma bayyana shawarar da ya taba samu daga wajen tsohon shugaban kasar na Najeriya kan siyasar Gombe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana shawarar da marigayi Muhammadu Buhari, ya ba shi kan siyasar jihar Gombe.
Farfesa Isa Pantami ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari, ya taɓa ba shi shawara da ya kauce wa shiga siyasar Gombe kai tsaye, domin a samu haɗin kai da zaman lafiya a jihar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Isa Pantami ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026 yayin da yake jawabi a sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar Gombe.

Kara karanta wannan
Atiku na shirin sake tsayawa takara, dan majalisa ya ba shi shawara kan siyasarsa
Farfesa Pantami ya je sakatariyar ne domin sabunta rajistar zamansa mamba na jam’iyyar APC.
Shawarar da Buhari ya ba Pantami
Tsohon ministan ya ce an ba shi wannan shawara ne a wa’adin farko na mulkin gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, domin tabbatar da fahimtar juna da kyakkyawar hulɗa a tsakanin shugabannin siyasar jihar.
“An yi hakan ne domin tabbatar da jituwa da kyakkyawar fahimta a cikin shugabancin siyasar jihar."
- Farfesa Isa Ali Pantami
A cewarsa, wannan shawara ta taimaka wajen ƙarfafa mutunta juna da fahimtar juna tsakaninsa da gwamnan jihar, jaridar Tribune ta dauko labarin.
“Tun daga lokacin, alaƙata da Gwamna Inuwa Yahaya ta kasance mai kyau. Babu wani sabani ko rashin fahimta a tsakaninmu har zuwa wannan lokaci."
- Farfesa Isa Ali Pantami
Ashe Sheikh Pantami ya dade a siyasa?
Tsohon ministan ya kuma jaddada cewa shigarsa siyasa ba sabon abu ba ne, yana mai cewa yana cikin harkokin siyasa tun shekarar 2001.
Ya bayyana cewa shiga siyasa na da hanyoyi daban-daban, yana mai kwatanta hakan da harkar tsaro.
“Siyasa, kamar harkar tsaro, tana da bangarori biyu: masu sanya kayan aiki da kuma waɗanda ba sa sanya su."
"Kamar yadda a fannin tsaro akwai hukumomi irin su DSS da NIA da ke aiki ba tare da kayan aiki ba, haka ma shiga siyasa na iya kasancewa ba tare da bayyanawa a fili ba. A wancan lokacin, muna daga cikin waɗanda ba sa sanya kayan aiki."
- Farfesa Isa Ali Pantami

Source: Facebook
Pantami ya kuma bayyana APC a matsayin jam’iyyar da ya taka rawa wajen gina ta, yana mai cewa yana daga cikin mutanen da suka fara tattaunawar da ta kai ga haɗewar jam’iyyun CPC da ACN, wanda daga bisani ya haifar da kafa jam’iyyar APC.
Jita-jitar auren Pantami da Aisha Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Ali Ibrahim Pantami, ya yi martani kan jita-jitar cewa zai auri Aisha Buhari.
Farfesa Pantami, wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi Buhari, ya bayyana rade-radin a matsayin kirkirarren labari mara tushe, yana mai cewa abin ya ba shi mamaki matuka.
Tsohon Ministan ya jaddada cewa Aisha Buhari uwa ce a gare shi da sauran wadanda suka yi aiki karkashin marigayi shugaban kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
