Atiku Na Shirin Sake Tsayawa Takara, Dan Majalisa Ya Ba Shi Shawara kan Siyasarsa
- Wani 'dan majalisar wakilai daga jihar Adamawa, Muhammad Basil, ya shiga sahun masu ba da shawara ga Atiku Abubakar
- Muhammad Basil ya bayyana cewa lokaci ya yi da tsohin mataimakin shugaban kasar zai koma dattijo mai ba da shawara a kasa
- 'Dan majalisar ya nuna kwarin gwiwar cewa jam'iyyar PDP za ta samu nasara a jihar Adamawa domin babu wata adawa mai karfi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai daga jihar Adamawa, Muhammed Basil, ya ba da shawara ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Hon, Muhammad Basil ya yi kira ga Atiku Abubakar, da ya janye daga siyasa tare da ɗaukar matsayi na dattijo mai ba da shawara a kasa.

Source: Twitter
'Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da jaridar The Punch ta wayar tarho.
Muhmmad Basil, wanda ke wakiltar mazabar Jada/Ganye/Toungo/Mayo-Belwa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne kimanin makonni biyu bayan ɗaya daga cikin ’ya’yan Atiku, Abba Atiku, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu.
Wace shawara dan majalisar ya ba Atiku?
'Dan majalisar ya ce lokaci ya yi da Atiku zai ja gefe domin bai wa matasa ’yan siyasa dama su jagoranci al’amura.
"Duk abin da mutum yake yi a rayuwa, akwai lokacin da ya kamata ya ja gefe ya bai wa matasa dama, musamman idan shekaru sun fara rinjaya."
- Muhammad Basil
Ya bayyana Atiku a matsayin ɗan siyasa mai karfi da kima, yana mai cewa kwarewarsa za ta fi amfani idan ya zama mai ba da shawara ga kasa, maimakon ci gaba da kasancewa cikin siyasar jam'iyya.
"Idan ka waiwayi baya ka ga yawancin waɗanda ku ka yi siyasa tare sun bar fagen, abu mafi dacewa shi ne ka sauka cikin mutunci ka zama jagoran siyasa ga matasa. Kujerar Atiku a matsayin dattijo mai ba da shawarwari na kasa tana jiransa.”
- Muhammad Basil
Atiku Abubakar ya samu yabo
Muhammad Basil ya jaddada cewa Atiku ya bayar da gudummawa mai yawa ga ci gaban Najeriya, yana mai cewa ficewa daga siyasa zai taimaka wajen kare mutuncinsa.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya fadi dalilan da suka sa ba zai yi shiru a kan harkokin gwamnati ba
"A kowane abu akwai lokacin da ribar sa ke raguwa. Shekaru na tafiya da sauri, kuma idan mutanen da ke kusa da kai suka fara komawa wasu bangarori, waɗannan alamu ne cewa ka kai wani matsayi a rayuwa.”
- Muhammad Basil

Source: Facebook
PDP za ta kai labari a Adamawa?
Dangane da damar PDP a Adamawa gabanin zaɓen 2027, Muhammad Basil ya ce jam’iyyar na nan da ƙarfinta kuma ba ta da abokin hamayya mai girma a jihar.
Basil yana wakiltar har da yankin Ganye, inda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fito.
“Ba a yin siyasa a shafukan jaridu ko kafafen yaɗa labarai kaɗai. Wasu suna magana tun safe zuwa dare, amma ranar zaɓe ba za ka same su a mazabunsu ba, domin ba su da mutane."
- Muhammad Basil
Atiku ya na zargin majalisa da niyyar magudi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi zarge-zarge kan majalisar dattawa.
Atiku ya ce majalisar dattawa ta shimfida hanya domin magudin babban zaben shekarar 2027 ta hanyar jinkirta gyaran dokar zabe ta 2022.
Ya ce gibin da ke cikin dokar zaben da ake amfani da ita a kasar nan ya taka rawa sosai wajen matsalolin da suka biyo bayan zaben 2023.
Asali: Legit.ng
