Kano Ta Kara Daukar Zafi, An Kalubalanci Kwankwaso kan Wasu Kwangilolin Gwamnatin Abba
- Zarge-zargen da tsohon hadimin gwamnan Kano, Sanusi Surajo Kwankwaso ya yi kan gwamnatin Abba Kabir Yusuf sun fara tayar da kura
- Hadimin gwamnan Kano, Salisu Yahaya Hotoro ya maida martani, inda ya jefa tambayoyi masu zafi ga kalaman na hannun daman Rabiu Kwankwaso
- Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamna Abba ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC mai mulki da Kwankwaso ke adawa da ita
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Musayar yawu ta fara zafi tsakanin magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da 'yan Kwankwasiyya kan kwangilolin gwamnatin jihar Kano.
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan kafafen sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ya kalubalanci 'yan Kwankwasiyya tare da jefa masu tambayoyi.

Source: Facebook
Hadimin Abba ya tankawa Sanusi Kwankwaso
Da yake hira da tashar Arewa Updates, Salisu Hotoro ya kalubalanci tsohon mai ba gwannan shawara kan al'amuran siyasa da aka kora kwanan nan, Sunusi Surajo Kwankwaso.
Wannan kalubale na zuwa ne biyo bayan ikirarin da ake yi na cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin godiya da butulci ga jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso.
Hotoro ya jefa wasu tambayoyi yayin da yake mayar da martani kan kalaman Sunusi Surajo Kwankwaso, yana mai cewa watakila bai san abin da ke faruwa ba ne.
Tun farko dai, Sanusi Surajo ya yi ikirarin cewa Gwamna Abba bai ba Kwankwaso wata kwangila ko wani nau'i na alfarma daga gwamnati ba tun da aka rantsar da shi.
Tambayoyin da aka jefawa tsagin Kwankwaso
Da yake bayyana wannan ikirari a matsayin karya da yunkurin yaudara, Salisu Hotoro ya ce suna da hujjojin da ke nuna cewa Kwankwaso da mabiyansa suna amfana da gwamnatin Abba.
Salisu Yahaya Hotoro ya ce:
"Wata kila shi Jagora Rabiu Musa Kwankwaso bai taba gaya wa Sunusi Surajo Kwankwaso cewa yana amfana da wannan gwamnatin ba, ina so ya je ya yi bincike, su waye ke gudanar da duka al'amuran da suka shafi aikin hajji.

Kara karanta wannan
Bayan Abba, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da APC kan sauya sheka? Gaskiya ta fito
"Na biyu, akwai kujeru guda 30 wadanda tun farkon gwamnatin nan, sai an dauke su an ba wa Kwankwaso, su wadannan kujeru ina ake kai su? Wa ake bai wa su?"
"Sannan ina so na tambaye shi, wanene ke aiwatar da shirin tura dalibai karatu? Kuma mutum nawa mai girma gwamna ya amince a tura, kuma nawa aka tura a zahiri? Shin tun da aka kafa gwamnati, wa ke kwangilar kawo dizal a ma'aikatar ruwa?
Hadimin gwamnan ya kuma tabo batun kwangilar sayo manyan injuna na biliyoyin Naira, wadanda har yanzu ba a riga fara aiki da su ba, da kuma sayen sinadaran tsaftace ruwa.

Source: Facebook
Kwankwaso ya amfana da Gwamnatin Abba?
Hotoro ya jaddada cewa ikirarin cewa Kwankwaso bai amfana da gwamnatin Abba Kabir ba, yunkuri ne na yaudarar jama'a don samun tausayawa.
Matashin wanda aka sani da jar hula a baya ya yi gargadin cewa idan masu wadannan zarge-zarge suka kasa ba da amsoshin tambayoyin da ya gabatar, to gara su yi shiru.
Ya kara da cewa gwamnati tana da hujjoji da za ta iya amfani da su wajen karyata duk wani labarin karya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Kwankwaso ya gana da Tinubu kan shiga APC?
A baya, kun ji cewa jam’iyyar NNPP ta musanta rahotannin dake cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya tattauna da Shugaba Bola Tinubu kan batun komawa APC.
Sakataren yaɗa labarai na NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya bayyana cewa duk waɗannan zarge-zarge ƙarya ce tsantsa da nufin ɓata sunan tsohon gwamnan na Kano.
Ladipo ya jaddada cewa, Kwankwaso ya gana da Shugaba Bola Tinubu ne tun a shekarar 2024, kuma ba su taɓa tattauna batun komawa APC ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

