Wike Ya Shiga Tsilla Tsilla, APC Ta Fadi Matsayinsa Wurinta kan Rigima da Fubara

Wike Ya Shiga Tsilla Tsilla, APC Ta Fadi Matsayinsa Wurinta kan Rigima da Fubara

  • Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya ce rikicin siyasa tsakanin Nyesom Wike da Siminalayi Fubara ba ya cikin hurumin jam’iyyar
  • Yilwatda ya bayyana cewa Wike dan jam’iyyar PDP ne, yayin da Fubara ke APC, don haka ba za su tsoma baki ba
  • Ya ce batun tsige Gwamnan Rivers al’amari ne na cikin APC, kuma jam’iyyar na da hanyoyin warware irin wadannan matsaloli

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya yi magana game da rikicin siyasar jihar Rivers da ke faruwa a yanzu.

Nentawe ya ce tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ba matsala ba ne ga APC, domin shi dan jam’iyyar PDP ne.

APC ta raba fada game da rigimar Wike da Fubara
Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike. Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Talata 3 ga watan Faburairun 2026 yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na tashar Channels Television.

Kara karanta wannan

An biyo kan masu shara: Gwamna ya yi barazanar korarsu kan rijistar zama yan APC

Yadda rigimar siyasar River ta yi kamari

A watan Disambar 2025 ne Wike ya fara yakin neman hana sake zaben Fubara, bayan ya zarge shi da karya yarjejeniyar da suka kulla kafin Shugaba Bola Tinubu ya dage dokar ta-baci a jihar Rivers.

Haka kuma, ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers da ke goyon bayan Wike sun zargi Fubara da kashe kudaden gwamnati ba tare da amincewarsu ba.

Daga bisani, ‘yan majalisar suka fara yunkurin tsige Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bisa zargin aikata manyan laifuka.

APC ta yi magana kan rikicin Wike, Fubara

Nentawe ya ce rikicin siyasa tsakanin Wike da Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, bai shafi jam'iyyar APC mai mulki ba.

Ya ce:

“Batun da ke tsakanin Wike da Fubara ba ya cikin hurumina a matsayina na shugaban APC na kasa. Wike yana PDP, Fubara kuma yana APC.”

Yadda APC ke warware matsalolin cikin gida

Shugaban APC ya kara da cewa ce-ce-ku-ce kan shirin tsige gwamnan Rivers ya shafi ‘yan jam’iyyar APC ne kawai da ke majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

APC ta sake taso da batun sauya shekar Kwankwaso zuwa cikinta, ta fadi tanadin da ta yi masa

Yilwatda ya kuma jaddada cewa ya dace a rika warware sabanin cikin gida cikin natsuwa da balaga, ba tare da fito da su fili ba.

“A lamarin tsige gwamna, ba Wike ba ne ake magana a kai yanzu. Maganar tana kan ‘yan majalisar dokokin APC. Wannan al’amari ne na cikin gida, kuma muna da hanyoyin warware irin wadannan matsaloli a jam’iyyar.
“Ba mu fitar da irin wadannan tattaunawa a bainar jama’a. Akwai hanyoyin cikin gida da ke bukatar balaga domin warware matsaloli."
APC ta ce Wike ba matsalarta ba ne a jam'iyya
Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

Wace matsala Wike zai jawo ga APC?

Da aka tambaye shi ko Wike matsala ne ga APC, Nentawe ya ce ko kadan ba zai zama matsala ba ga jam'iyyar.

Nentawe ya amsa da cewa:

“A’a, ko kadan.”

Dalilin hana Wike shiga filin wasan Rivers

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Rivers ta ce ba ta hana Nyesom Wike shiga filin wasa ba, ta bayyana cewa babu wata takardar neman izini daga gare su.

An ce ana ci gaba da gyare-gyare a filin wasan kuma ba shi da aminci ga taron jama’a, lamarin da ya sa aka hana duk wani taro.

Gwamna Simi Fubara ya jaddada goyon bayansa ga Bola Tinubu, yana cewa gwamnatin Rivers na sahun gaba wajen tallafa wa sake zaɓensa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.