Gwamna Abba da Gwamnonin da Suka Koma APC Za Su Yi Tasiri a 2027? CERON Ta Yi Bayani
- Kungiyar CERON ta gargadi jam'iyyar APC mai mulki da cewa yawan gwamnoni ba shi zai tantance yadda zaben 2027 zai kaya ba
- Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnoni ke barin jam'iyyunsu, suna komawa APC gabanin babban zaben 2027
- CERON ta ce 'yan Najeriya sun waye kuma babu tabbacin gwamnonin za su iya tasiri idan aka fita kada kuri'a a zabe na gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kungiyar Campaign for Equal Rights and Opportunities for all Nigerians (CERON) ta yi magana kan gwamnonin da ke tururuwar komawa jam'iyyar APC.
Kungiyar, mai fafutukar kare hakkin 'yan Najeriya ta bayyana cewa komawar gwamnonin jihohi APC mai mulki ba zai tantance sakamakon zaɓen 2027 ba.

Source: Twitter
Gargadin da CERON ta yi wa APC

Kara karanta wannan
An fara nuna wa juna yatsa kan wanda ya shirya katin rijistar Bello Turji a jam'iyyar APC
Vanguard ta rahoto cewa kungiyar ta gargadi APC da kada kwarin gwiwarta ya wuce gona da iri saboda ta ga gwamnoni na rige-rigen shiga cikinta.
Ta jaddada cewa gwamnonin da ke barin jam’iyyunsu zuwa APC ba sq nuna tabbacin samun nasara ba ne a zaɓen gaba.
CERON ta bayyana matsayarta ne a cikin wata sanarwa da sakatarenta, Mista Francis Odiir, ya fitar a ranar Litinin, a daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauyen siyasa a faɗin ƙasar.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na jihar Taraba, Agbu Kefas na cikin gwamnonin da suka koma APC a baya-bayan nan.
CERON ta ce yan Najeriya sun waye
A cewar Odiir, sauya sheƙar gwamnonin na iya zama mara tasiri kan yadda ‘yan Najeriya za su kaɗa ƙuri’arsu a 2027, musamman idan aka gudanar da zaɓen cikin adalci da gaskiya.i
Sanarwar ta ce:
“Abu ne da ya zama ruwan dare ga ‘yan siyasar Najeriya su rika sauya jam’iyya a tsakiyar wa’adinsu, galibi saboda son kai, kamar yadda muke gani a yanzu,” in ji Odiir.
“Ba su fahimci irin wayewar kai da ‘yan Najeriya suka samu a wannan lokaci ba. Matakin fahimtar jama’a a yanzu ya zarce tunanin mutane da dama.”

Source: Twitter
CERON ta hango dalilin masu sauya sheƙa
Kungiyar ta yi nuni da cewa yawancin sauya sheƙar gwamnonin ya samo asali ne daga rikicin da ke addabar jam’iyyar adawa ta PDP, ba wai saboda ƙaunar APC ba, cewar rahoton Daily Post.
“Gaskiyar magana ita ce, gwamnoni na sauya sheka ne akamakon rikicin PDP. Ba wai suna son APC ba ne, suna guduwa ne daga gidan da ke rushewa don neman mafaka a wani wuri da shi ma ba tabbas,” in ji Odiir.
Shettima ya karbi gwamnan Taraba zuwa APC
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya karbu gwamnan Taraba, Agbu Kefas, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Shettima ya bayyana sauya shekar a matsayin abin alfahari ga jam’iyyar da kuma kasa baki daya, inda ya yabawa Kefas bisa salon shugabancinsa na hadin kai.
Mataimakin shugaban kasar ya yabawa Kefas kan fahimtarsa game da bambancin kabilu da addinai a Taraba, tare da kokarinsa na karfafa hadin kai a jihar.
Asali: Legit.ng
