'Abin da Ya Kamata Atiku Ya Yi Wa Peter Obi kan Tikitin ADC a Zaben 2027'
- An bukaci Atiku Abubakar, da ya goyi bayan Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a babban zabe mai zuwa na 2027
- Jagoran Obidient Movement na kasa, Yunusa Tanko Yakasai, ya jaddada muhimmancin Peter Obi a daidai lokacin da ake muhawara kan makomar ADC da alkiblarta a siyasa
- Magoya bayan Obidient da ke da ra’ayi mabambanta sun dage kan cewa Peter Obi ne kadai zabinsu a zaben da za a yi a farkon shekarar badi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jagoran kungiyar Obidient na kasa, Yunusa Tanko, ya yi tsokaci kan burin Atiku Abubakar da Peter Obi na yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Mista Yunusa Tanko ya bayyana cewa ya kamata Atiku Abubakar ya marawa Peter Obi baya domin ya samu damar darewa kan kujerar mulkin Najeriya.

Source: Twitter
Yunusa Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics On Sunday' na tashar TVC a ranar Lahadi, 1 ga watan Fabrairun 2026.
Me Jagoran Obidient ya ce kan Atiku?
Ya ce Atiku Abubakar na iya mara wa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, baya tare da "nada shi” domin ya rike tutar ADC a babban zaben 2027.
Jagoran na Obidient ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan muhawarar da ke gudana game da tikitin shugaban kasa na ADC a 2027, da kuma rawar da manyan ’yan adawa za su taka gabanin zaben.
Yayin da ake tambayarsa abin da zai faru idan Atiku ya hana Peter Obi samun tikitin ADC, Yunusa Tanko ya yi watsi da yiwuwar hakan, inda ya bayyana Atiku a matsayin jagora kuma uba.
"Atiku Abubakar jagora ne kuma uba ne. Ba zai taba shiga irin wannan wasan ba.”
- Yunusa Tanko Yakasai
An ba Atiku shawara kan Peter Obi
A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban kasar na da ’yancin tsayawa takara, amma kuma yana da ’yancin goyon bayan wani dan takara idan hakan zai kara wa jam’iyyar damar yin nasara.

Source: Facebook
"Yana da ’yancin tsayawa takara, haka kuma yana da ’yancin zabar wani. Wannan na cikin hakkinsa na dan Adam a matsayin uba da ke son yin nasara."
"Nasara ba ta nufin sai ni da kaina na yi. Nasara na iya kasancewa in kama ka in ce je ka ci mana zabe, na san kana da kwarewa. Wannan abu ne mai yiwuwa."
- Farfesa Yunusa Tanko
Wadannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara tattaunawa a tsakanin ’yan adawa kan tikitin shugaban kasa na jam’iyyar ADC, yayin da magoya bayan Peter Obi ke ci gaba da kira ga shugabannin jam’iyyar da su tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na 2027.
Shirin Peter Obi kan zaben 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya yi magana kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Peter Obi wanda ya zo na uku a zaɓen 2023 ya ayyana cewa zai fafata a 2027 don neman kujerar da shugaban kasa Bola Tinubu yake a kai.
Tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana cewa ba shi da niyyar zama abokin takarar kowa a babban zaɓen ƙasar nan dake tafe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


