Abin da Ganduje da makusantan Gwamna Abba Suka Tattauna a Abuja
- Tsohon Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya karɓi bakuncin Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Abuja da hadimin Gwamnan Kano Sanusi Bature D-Tofa
- Matasan 'yan siyasan biyu sun kai wa tsohon Gwamna Ganduje ziyarar a gidansa bayan 'yan kwanaki da sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC
- A yayin ziyarar, an tattauna batun ƙarfafa APC da ci gaban ƙaramar hukuma, lamarin da ya jaddada muhimmancin haɗin kai da shugabanci nagari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mai Girma tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya karɓi bakuncin makusantan Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Mukhtar Bello Dan Maliki, tare da mai magana da yawun gwamnan jihar kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, sun kai wa Ganduje ziyara a gidansa da ke Abuja.

Source: Facebook
Tsohon Kwamishinan yada labarai a gwamnatin baya da Ganduje ya jagoranta, Kwamred Muhammad Garba ne ya tabbatar da haka ta cikin wani sako sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Makusantan Abba sun ziyarci Ganduje
Sanarwar ta ce an kai ziyarar a wani muhimmin mataki na siyasa, musamman domin ƙarfafa haɗin kai a yankin Dawakin Tofa, ƙasar da tsohon gwamnan ya fito, da kuma daidaita sahu a tsarin jam’iyyar APC a wannan yanki.
Ta kara da cewa sn tattauna ci gaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, inganta shugabanci, da tabbatar da zaman lafiya ga al’ummar jihar Kano.
Sanarwar ta kara da cewa sanawar ta nuna muhimmancin jagoranci da kishin jam’iyya wajen tabbatar da dorewar APC a siyasance, musamman a matakin ƙananan hukumomi.
Masu halartar taron sun jaddada cewa haɗin kai tsakanin shugabanni na da matuƙar tasiri wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a cikin al’umma.
An fahimci juna a ganawar su Ganduje
Sanarwar da Muhammad Garba ya sanya wa hannu ta kara da cewa ziyarar ta ƙara haskaka matsayin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin dattijo kuma uba a siyasar Kano.
Ta ce a cewar wasu daga cikin mahalarta, irin wannan ganawa na taimakawa wajen daidaita fahimta da kauce wa sabani a harkokin jam’iyya.

Source: Facebook
Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Mukhtar Bello Dan Maliki, ya bayyana godiyarsa bisa tarbar da aka yi masu a gidan Ganduje.
Ya kara da cewa shawarwarin da suka samu daga tsohon gwamnan za su taimaka matuƙa wajen inganta ayyukan mulki da hidima ga jama’ar ƙaramar hukumar.
An gano wanda ya kwarmata 'rashawar' Ganduje
A baya, mun wallafa cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya zargi wani fitaccen dan kasuwa kan tona masa asiri da jifansa da zargin badakala.
Ganduje na zargin Ahmad Rabiu, da cewa shi ne ya yada wasu takardun sirri ga jaridu, zargin da aka ce ba gaskiya ba ne, wanda ya alakanta shi da almundahana.
Wadannan takardu sun bankado wata badakala ta biliyoyin Naira da ta shafi mallakar Kamfanin tashar sandauri a lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje a Kano.
Asali: Legit.ng


