Ministan Tsaro zai Rikide zuwa Siyasa bayan Gwamnatin APC Ta ba Shi Mukami

Ministan Tsaro zai Rikide zuwa Siyasa bayan Gwamnatin APC Ta ba Shi Mukami

  • Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa yana shirin tsunduma a cikin harkokikin siyasa domin a dama da shi
  • Christopher Musa ya kara da cewa jam'iyyar APC ta ba shi dandali tun daga lokacin da yake a matsayin Shugaban hafsoshin tsaro har zuwa yanzu
  • Tsohon Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya ya ce Shugaba Bola Tinubu ya cancanci cikakken goyon baya, har da wa’adin mulki na biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana cewa yanzu haka yana kokarin rikidewa zuwa harkokin siyasa a Najeriya.

Janar Christopher Musa, wanda ya rike mukamin babban hafsan tsaron Najeriya ya ce akwai yiwuwar ya shiga jam’iyyar APC a hukumance.

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare: Babban alkalin Katsina ya tsage gaskiya kan batun sakin 'yan bindiga 70

Christopher Musa zai shiga harkokin siyasa
Janar Christopher Musa tare da Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: HQ Nigerian Army/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ministan tsaron ya yi wannan bayani ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na Channels Television.

Babban Ministan tsaro zai shiga siyasa

Peoples Gazette ta ruwaito cewa duk da bai gama canja wa daga matsayarsa zuwa cikakken 'dan siyasa ba, amma yana dab da shiga cikinta.

A yayin hirar, an kuma tambayi Janar Musa ko a yanzu haka 'dan jam’iyyar APC mai mulki. ne, sai ya ce:

"Tukunna dai, amma ina ganin zan shiga. Tabbas. APC ta ba ni dandali tun daga lokacin da nake CDS har zuwa yau, don haka me zai hana shiga cikinta?”
Janar Christopher Musa zai koma APC
Ministan tsaron Najeriya yayin shan rantsuwar kama aiki, Shugaba Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ministan ya kara da cewa Shugaba Bola Tinubu ya cancanci cikakken goyon baya daga kowane bangare, yana mai jaddada cewa a shirye yake ya taimaka wa gwamnatin ta kowace hanya da zai iya.

Ministan tsaro zai taimaka Tinubu ya zarce

Ministan tsaron ya kara da cewa ba shi da dalilin da zai ki goyon bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi wa'adi na biyu a mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya na cikin alheri, sun fara cewa arahar abinci ta yi yawa a mulkin Tinubu'

Ya ce:

“Shugaban kasa yana bukatar dukkannin goyon baya, gaba daya. Zan ba shi dukkannin goyon bayana, duk abin da zan iya yi don tabbatar da cewa ya yi nasara a aikin da aka dora masa, har da matsawa gaba zuwa wa’adi na biyu. Ina ganin zan yi iyakar kokarina.”

Janar Musa mai shekaru 58 ya rike mukamin Babban Hafsan Tsaro ne 18 daga ranar 23 ga Yuni, 2023, zuwa ranar 30 ga Oktoba, 2025, kafin ya yi ritaya.

Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da shi a matsayin Ministan Tsaro a fadar Aso Villa a ranar 4 ga Disamba, 2025.

Kalaman Janar Musa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC tun bayan da Shugaba Tinubu ya karbi ragamar mulki a watan Mayu, 2023.

Yadda Ministan tsaro ya samu mukami a Amurka

A baya, mun wallafa cewa tsohon Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ya samu babban mukami a ƙasar waje bayan ritayarsa daga aikin soja.

Kara karanta wannan

Sai Tinubu: 'Dan Atiku ya sha alwashi, za a hadu da shi a kada mahaifinsa a 2027

An nada Janar Musa a matsayin ɗaya daga cikin 'yan majalisar gudanarwa ta Midlothian Angel Network (Midlo), wata cibiyar Amurka da ke da alaka da tsaro tsakanin kasar da Afrika,

Rahotanni sun nuna cewa Midlo wata cibiyar saka jari ce ta angel investors da ke aiki domin tallafa wa sababbin kamfanoni masu tasowa, tare da haɗa masu zuba jari daga sassan duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng