‘Babu Gwamnan da Zai Zauna a NNPP’: An Fadi Babban dalilin Abba na Shiga APC
- Kwamishina a gwamnatin Abba Kabir ya bayyana dalilin ficewar mai gidansa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki
- Ibrahim Waiya ya ce rikicin cikin gida ya lalata NNPP da canjin tambari daga kwandon ’ya’yan itatuwa zuwa littafi ne ya haddasa matsalar
- Waiya ya ce gwamna Abba Yusuf ya fice daga NNPP ne saboda rashin tabbas da kararraki da ke kotu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya yi magana kan siyasar Kano.
Ibrahim Waiya ya bayyana cewa ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC ba cin amana ba ce, illa tilas.

Source: Twitter
A wata hira da Vanguard ta bibiya, Waiya ya ce makomar NNPP ta kasance cikin duhu saboda mummunan rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar tun bayan kafa ta.
Ya bayyana cewa a farko tambarin NNPP kwandon kayan marmari ne, amma daga bisani aka yi yunƙurin sauya shi zuwa littafi ba tare da tuntubar wandanda suka kafa jam’iyyar ba.
Yadda rikicin NNPP ta farraka ta a Kano
A cewarsa, rikicin NNPP ya kai matakin da ake da shugabanni daban-daban a Kano, ciki har da Hashim Dungurawa, Rabiu Kwankwaso da Elmasud Doguwa.
Ya ce har bangaren kwandon ’ya’yan itatuwa ya taba dakatar da gwamnan Kano, duk da kasancewarsa shi kaɗai gwamnan da jam’iyyar ta samar.
Waiya ya ce hakan ya nuna a fili cewa jam’iyyar tana fama da babbar matsala wacee ke barazana ga wanzuwarta a siyasance da kuma a doka.
Ya ce:
“Ta yaya za ka zauna a jam’iyya irin wannan, alhali ba ka da tabbacin makomarka?”
Ya ce su kansu sun san cewa NNPP ba ta da cikakken tushe a doka, kuma a nan gaba ba za a iya gane ta a hukumance ba.

Source: Facebook
Abubuwan da suka dagula NNPP
Kwamishinan ya kara da cewa har wanda ya kafa jam’iyyar, Boniface, ya sha nuna rashin jin dadinsa kan sauyin tambari a wurare daban-daban.
A cewarsa, akwai bangaren NNPP na Boniface da kuma bangaren Kwankwasiyya, lamarin da ya kara raba jam’iyyar gida biyu.
Ya tuna cewa wannan rikici ne ya sa wasu jiga-jigan jam’iyyar kamar Hon. Ali Madaki da Alhassan Rurum suka fice daga NNPP.
Da aka tambaye shi ko Kwankwaso bai san duk wadannan matsaloli ba, Waiya ya ce tsohon gwamnan Kano yana da cikakken sani game da hukuncin kotuna.
Ya ce babu yadda za a yi a bukaci gwamna ya ci gaba da zama a jam’iyyar da ke fama da irin wannan rikici mai tsanani.
Waiya ya ce ba wannan ne karo na farko da ake samun sauyin sheka a siyasar Najeriya ba, yana mai tunatar da cewa Kwankwaso ma ya taba ficewa a baya.
Ya ce:
“Shi ma Kwankwaso gwamna ne lokacin da ya fice tare da magoya bayansa zuwa APC.”
Ya ce kwatankwacin wannan ne ke faruwa a yanzu, inda gwamna Abba Yusuf ya koma APC tare da mabiyansa.
APC ta yiwa Kwankwaso martani kan zaben Abba
Mun ba ku labarin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC za ta hana shi samun nasara a zaɓen 2027.
Jam’iyyar APC ta yi watsi da wannan hasashe, tana mai cewa goyon bayan Abdullahi Ganduje zai tabbatar wa gwamnan nasara a zaɓe.
Sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf ta ƙara zafafa yanayin siyasa a Kano, inda ake ci gaba da sauya layi da matsaya a fadin jihar.
Asali: Legit.ng


