Bayan Shigar Gwamna APC, Shettima Ya Tura Roko ga Gwamnonin PDP 2 a Arewa

Bayan Shigar Gwamna APC, Shettima Ya Tura Roko ga Gwamnonin PDP 2 a Arewa

  • Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana sauya sheƙar Gwamna Agbu Kefas zuwa APC a matsayin abin alfahari
  • Shettima ya ce APC ta ƙara ƙarfi a Arewa maso Gabas, yana fatan gwamnoni a Adamawa da Bauchi za su sake duba matsayinsu
  • Gwamna Kefas ya ce ya koma APC ne domin ci gaban Taraba, yana yaba wa Shugaba Tinubu da ajandar Renewed Hope mai sauya ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana jin dadinsa game da sauya sheƙar Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas.

Shettima ya ce sauya shekar Kefas zuwa jam’iyyar APC a matsayin abin alfahari da ya taba zuciyarsa ƙwarai.

Shettima ya roki gwamnonin PDP 2 su dawo APC
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayin taron majalisar zartarwa. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Yadda APC ke samun ƙarfi a Arewa

Shettima ya yi wannan jawabi ne a Jalingo, babban birnin Taraba, yayin bikin tarba na musamman da aka shirya domin maraba da gwamnan cikin jam’iyya mai mulki, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

APC ta kara karfi, Shettima ya karbi gwamnan da ya shiga jam'iyyar a hukumance

Ya ce wannan sauya sheƙa ta ƙara wa APC ƙarfi, musamman a yankin Arewa maso Gabas, inda yanzu jam’iyyar ke da gwamnoni da dama.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya nuna fata cewa gwamnoni a jihohin Adamawa da Bauchi za su, a lokaci mai dacewa, sake duba matsayinsu su mara wa APC baya.

A wajen taron, Shettima ya ayyana Gwamna Kefas a matsayin jagoran APC a Taraba, tare da kiran mambobin jam’iyyar su mara masa baya.

Ya ce goyon bayan jam’iyya zai ƙarfafa gwamnan wajen haɗa kan al’ummar jihar da kuma samar da ribar dimokuraɗiyya ga jama’a.

Gwamna Kefas ya koma APC a hukumance
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayin karbar Gwamna Agbu Kefas na Taraba zuwa APC. Hoto: Agbu Kefas.
Source: Facebook

Musabbabin komawar Gwamna Kefas APC

Tun da farko, Gwamna Kefas ya ce shawarar komawa APC, tare da ‘yan majalisar ministocinsa da ‘yan majalisa, ba ta siyasa ba ce illa neman ci gaban Taraba.

Ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaba mai hangen nesa, yana cewa ajandarsa ta Renewed Hope ta cancanci goyon baya daga dukkan masu kishin ƙasa.

Gwamnan ya tabbatar wa mutanen Taraba cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi jama’a kai tsaye.

Kara karanta wannan

Bayan shigowar Abba, Ganduje ya faɗi dacen da aka yi na samun Tinubu a Najeriya

Haka kuma, Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce sauya sheƙar Kefas babbar dabara ce da ta amfani al’ummar Taraba.

Ya ce Taraba jiha ce mai albarkatu masu yawa, kuma shigarta APC alama ce ta sabon babi na ci gaba da farfaɗowa, cewar Punch.

Yilwatda ya kuma yi kira ga sauran gwamnoni a PDP da su sake tunani, su shiga abin da ya kira tafiyar cigaban kasa.

Shettima ya kaddamar da gidaje a Tudun Biri

An ji cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da sababbin gidaje `133 a Tudun Biri domin sake tsugunar da mutanen garin.

Gwamnatin Tarayya ta gina makarantu da sauran ababen more rayuwa a matsayin cika alkawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi a baya.

Wannan aiki na Tudun Biri yana daga cikin shirin gwamnati na sake gina yankunan da rikici ya shafa, musamman a wasu jihohi 7 na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.