Bayan Abba, Kwankwaso Ya Shiga Tattaunawa da APC kan Sauya Sheka? Gaskiya Ta Fito
- Jam’iyyar NNPP ta musanta rahotannin dake cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya tattauna da Shugaba Bola Tinubu kan batun komawa APC
- Kakakin NNPP ya bayyana cewa masu yada jita-jitar suna son bata sunan Kwankwaso ne bayan sauya shekarar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf
- Jam'iyyar ta jaddada cewa Kwankwaso ya gana da shugaban kasa ne tun a shekarar 2024 kuma tattaunawarsu ba ta shafi sauya sheka ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Jam’iyyar NNPP ta fito fili ta karyata rahotannin dake cewa jagoranta na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nemi kulla yarjejeniyar komawa APC mai mulki.
Wannan martani na zuwa ne bayan ficewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya haddasa jita-jitar cewa Kwankwaso ma ya yi yunkurin bin sa amma aka samu saɓani saboda wasu "tsauraran buƙatu" da ya gabatar.

Source: Twitter
"Kwankwaso ya yi kuskuren lissafi" - Baba
Baba Yusuf, babban jami'i a kamfanin Global Investment and Trade, ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Arise TV cewa Kwankwaso ya yi kuskuren lissafin tasirinsa a siyasance yayin tattaunawar da aka zarga ya yi da APC.
Yusuf ya kafa hujja da cewa ficewar Abba Gida-Gida ya rage wa Kwankwaso ƙarfin iko a siyasance, musamman ganin cewa gwamnan surukinsa ne.
Haka kuma jami'in kamfanin ya ce kowa ya san Abba amintaccen ɗalibin Kwankwaso ne na siyasa wanda yanzu ya koma ɓangaren babban abokin hamayyarsa, Abdullahi Umar Ganduje.
"Kwankwaso bai tattauna da APC ba" - NNPP
Sakataren yaɗa labarai na NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya bayyana wa jaridar Punch cewa duk waɗannan zarge-zarge ƙarya ce tsantsa da nufin ɓata sunan tsohon gwamnan na Kano.
Ladipo ya jaddada cewa, Kwankwaso ya gana da Shugaba Bola Tinubu ne tun a shekarar 2024, kuma ba su taɓa tattauna batun komawa APC ba.
Ya kuma ce masu yaɗa jita-jitar suna yin hakan ne domin su raba Kwankwaso da sauran ƴan adawa masu ƙoƙarin haɗa ƙarfi da ƙarfe.
Johnson ya bayyana Kwankwaso a matsayin mutum mai nagarta wanda ke yin siyasarsa domin amfanin talakawa, ba don neman muƙami ba.

Source: Twitter
Darussan siyasa daga sauran jihohi
Baba Yusuf dai ya yi nuni da cewa abin da ke faruwa da Kwankwaso a Kano ba baƙon abu ba ne, inda ya kwatanta hakan da rikicin siyasa dake faruwa a Jihar Rivers, da kuma saɓanin da aka samu a baya tsakanin Gwamna Obaseki da wasu iyayen gidan siyasa.
Ya bayyana cewa wannan wani darasi ne ga ƴan siyasa cewa sau da yawa bukatar yin wasan dogon zango ta fi cin gajiyar yanzu-yanzu.
Amma a ɓangaren NNPP, jam'iyyar ta tsaya tsayin daka cewa Kwankwaso yana nan daram a matsayinsa na jagoran adawa.
Jinkirin komawar Kwankwaso ADC
A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata Rabiu Kwankwaso na jinkirta komawa jam’iyyar ADC saboda rashin tabbacin makomar Peter Obi a zaben 2027.
Hakan bai rasa nasaba da rahotannin da ke cewa akwai yarjejeniya kan hadakar Obi da Kwankwaso game da zaben 2027.
Wasu shugabannin Arewa sun gargadi Kwankwaso kada ya gaggauta ficewa NNPP har sai an tabbatar da Obi zai samu tikitin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng


