Doguwa Ya Karbi Manyan Jiga Jigai, Kwankwaso Ya Rasa Wasu Magoya Baya a Kano
- Jam'iyyar APC na ci gaba da karbar mukarraban Gwamna Abba Jabir Yusuf bayan ya sauya sheka daga NNPP a jihar Kano
- Hon. Alhassan Ado Doguwa ya karbi kwamishina, shugaban karamar hukuma da manyan jiga-jigan NNPP da suka koma jam'iyyar APC
- Dan Majalisar wakilai ya ce sun yi maraba da matakin Gwamna da mukarrabansa kuma za su yi aiki tare domin nasarar APC a zabuka masu zuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya karbi daruruwan mambobin jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a jihar Kano.
Wannan mataki ya zama wani ci gaba ga jam'iyyar APC, wanda ke nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da kuma gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Twitter
Doguwa ya karbi jiga-jigai zuwa APC
The Nation ta ce Doguwa, wanda ke wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a majalisar tarayya, ya jagoranci aikin rajistar mambobin APC inda ya karbi manyan masu sauya sheka daga NNPP.
Daga ciki har da Kwamishinan Ruwa na jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, da wasu jami’an gwamnati.
'Dan majalisar tare da masu sauya shekar sun yi rajistar zama mambobi ta intanet, sannan suka yi wani gangami na kaddamar da yakin neman zaben tazarce na Shugaba Tinubu da Gwamna Abba.
Ado Doguwa zai hada kai da Gwamna Abba
Hon. Doguwa ya ce:
"Dukkanmu mun shirya aiki tare don maslahar APC a karkashin jagorancin Shugaba Tinubu a matakin tarayya, da Gwamna Abba a matakin jiha, kamar yadda yake kunshe a cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu.
"Mun amshi wannan ci gaba da kyakkyawar zuciya kuma mun yi imanin cewa nasara ce ga daukacin mambobin jam’iyyar. Yanzu mu abokan tafiya ne a shirin mai girma gwmana na Kanoce ta daya."
Doguwa ya ce manyan mutanen da suka sauya shekar sun hada da Kwamishinan Ruwa kuma tsohon shugaban APC na jiha, Alhaji Umar Haruna Doguwa; da Injiniya Ado Ibrahim Doguwa.

Kara karanta wannan
Bayan Kano ta koma hannun APC, Tinubu ya fadi wanda zai zama jagoran jam'iyya a jihar
Sauran sun hada da Shugaban Karamar Hukumar Doguwa, Abdul Rashid Doguwa, tare da daukacin majalisar zartarwarsa da ta dokoki, kamar yadda Punch ta kawo.
Yadda Gwamna Abba ya shiga APC
Wannan sauya sheka na zuwa ne bayan da shi kansa Gwamna Abba ya riga ya shiga jam'iyya mai mulki, APC.
Gwamna Abba ya sauya sheka ne bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Tinubu, wadda aka yi amanna cewa ta warware takaddamar da ke tattare da yunkurin shigarsa APC.

Source: Facebook
Daga ciki har da batun tikitin takarar gwamna wanda tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya tabbatar da cewa gwamnan ne zai sake yi takara a 2027, tare da kira ga sauran masu neman takara da su janye masa.
Gwamnatin Kano ta kafa hujja a rikicin NNPP
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ikirarin da ta yi a kan rigingimun cikin gida na jam'iyyar da ta bari, NNPP ya kara fitowa sarari.
Mai magana da yawun gwamna, Sanusi Bature D-Tofa ya ce yadda NNPP ta gabatar da ’yan takara uku daban-daban ga INEC a zaben cike gurbin da za a yi ya kara nuna rikicin jam'iyyar.
A cikin wata sanarwa, Sanusi Bature D-Tofa ya kara tabbatar da ikirarin da suka yi na cewa jam’iyyar na fama da rikicin cikin gida mai tsanani.
Asali: Legit.ng
