Matawalle Ya Fadi Abin Zai ba Tinubu Damar Cin Zabe cikin Sauki a 2027
- Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaben 2027
- Matawalle ya ce manufofin Tinubu sun fara haifar da daidaiton tattalin arziki, inganta tsaro da karfafa cibiyoyin gwamnati musamman a Arewa
- Ya gargadi ‘yan siyasa masu shirya rikici da cewa burinsu na kashin kai na iya lalata dimokuradiyya, yana kira da a goyi bayan shirye-shiryen gwamnati
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Karamin Ministan Harkokin Tsaro, Dakta Bello Matawalle, ya bayyana cikakken kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi nasara a 2027.
Matawalle ya ce Tinubu zai samu nasara mai gamsarwa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027, yana kira ga ‘yan Najeriya da masu ruwa da tsaki a siyasa da su mara masa baya.

Source: Original
Gargadin Matawalle ga 'yan siyasa a Najeriya
Matawalle ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Abuja, inda ya ce salon jagoranci da manufofin Shugaba Tinubu sun sanya kasar nan kan turbar daidaiton tattalin arziki, karfafa hukumomi da kuma dunkulewar kasa, cewar Punch.
Ministan ya gargadi ‘yan siyasa da ke shiga shirye-shiryen makircin siyasa tun da wuri da kuma fafutukar karbe mulki, yana cewa irin wadannan dabaru na da illa ga kwanciyar hankalin dimokuradiyyar Najeriya.
A cewarsa:
“Shugaba Tinubu ya dauki matakai masu karfi domin daidaita tattalin arziki da karfafa cibiyoyin kasa.
Wadanda ke shirya kifar da shi suna aiki ne saboda muradunsu na kashin kai, ba don amfanin jama’a ba.”
Matawalle ya kara da cewa idan aka ba Shugaba Tinubu damar kammala shirye-shiryen da yake yi na gyara, babu shakka zai samu gagarumar nasara a zaben 2027.
Ya ce tasirin manufofin Shugaban kasar ya riga ya fara bayyana a fadin Najeriya, musamman a yankin Arewa, inda aka samu ingantaccen shugabanci, daukar matakan tsaro da kuma gyaran hukumomi kamar yadda zancen ya zo a Tribune.

Kara karanta wannan
Sanata Ndume ya dauko da zafi, ya tona asirin wasu hadimai na kusa da Shugaba Tinubu

Source: Original
Matawalle ya roki yan Najeriya game da Tinubu
Ministan ya bukaci ‘yan siyasa da su rungumi tattaunawa mai ma’ana da hadin kai maimakon amfani da dabarun rarrabuwar kawuna, yana jaddada cewa muradin kasa ya fi kowanne buri na kashin kai muhimmanci.
Haka kuma, Matawalle ya roki ‘yan Najeriya da su goyi bayan manufofin gwamnati da ke da nufin bunkasa tattalin arziki mai dorewa, inganta tsaro da kuma karfafa hadin kan kasa.
Ya ce:
“Maimakon fadawa rikice-rikicen siyasa da tunani na gajeren lokaci, ya kamata mu mayar da hankali kan hanyoyin samar da ayyukan yi, tsaro da cibiyoyi masu karfi domin amfanin ‘yan Najeriya.”
An shawarci Tinubu ya rike Matawalle
A wani labarin an ji ana ci gaba da kiraye-kiraye ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sauke karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle daga mukaminsa.
Masu yin kiraye-kirayen dai suna yi ne bisa zargin cewa tsohon gwamnan na Zamfara yana da alaka da 'yan bindiga.
Sai dai, kungiyar NSCI ta fito ta ba Shugaba Tinubu shawarar abin da ya kamata ya yi wa karamin Ministan na tsaro inda ta bukaci ya ci gaba da rike shi a mukamin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
