APC Ta Kara Karfi, Shettima Ya Karbi Gwamnan da Ya Shiga Jam'iyyar a Hukumance
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu karuwa bayan shigowar gwamnan jihar Taraba zuwa cikinta a hukumance
- Gwamna Agbu Kefas ya samu tarba daga wajen Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sauran jiga-jigan jam'iyyar APC
- Shettima ya yi jawabai a wajen karbar Gwamna Kefas zuwa APC, ya ce ya ji dadin matakin da ya dauka na shiga jam'iyya mai mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya sanar da sauya sheka a hukumance daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Gwamna Agbu Kefas ya samu tarba daga wajen Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, yayin wani taro da aka gudanar a birnin Jalingo.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Shettima ya karbi gwamnan ne zuwa APC a madadin Shugaba Bola Tinubu, a ranar Asabar, 31 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan
Bayan Kano ta koma hannun APC, Tinubu ya fadi wanda zai zama jagoran jam'iyya a jihar
Shettima ya karbi Gwamna Kefas zuwa APC
Shettima ya bayyana sauya shekar a matsayin abin alfahari ga jam’iyyar da kuma kasa baki daya, inda ya yabawa Kefas bisa salon shugabancinsa na hada kai da kuma jajircewarsa wajen kawo ci gaba, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
Ya ce APC an kafa ta ne a matsayin dandali ga ’yan Najeriya masu kishin ci gaba, yana mai cewa matakin da gwamnan Taraba ya dauka na shiga jam’iyyar ya zo a kan lokaci kuma ya dace da tushen akidun APC.
"Mun yi amanna cewa kasashe na dorewa ne idan sun gane karfinsu. Jihar Taraba muhimmin bangare ne na Najeriya, wadda Allah Ya albarkace ta da dimbin damar ci gaban kasa."
“An gina APC a matsayin wurin haduwar mutanen da suka kuduri aniyar kawo ci gaba. A yau, abin alfahari ne ganin Taraba ta shigo wannan gida. Muna maraba da dan’uwanmu gida, domin a gaskiya, tun tuni yana tare da mu."

Kara karanta wannan
Sanusi II ko Aminu Ado: Gwamna Abba ya bayyana wanda zai ci gaba da zama Sarkin Kano
- Kashim Shettima
Shettima ya yabawa Gwamna Kefas
Shettima ya yabawa Kefas kan fahimtarsa game da bambancin kabilu da addinai a Taraba, tare da kokarinsa na karfafa hadin kai a jihar, yana kuma kira ga al’ummar Taraba da su mara wa gwamnan baya domin kawo ci gaba.
“Muna alfahari da Gwamna Agbu Kefas saboda salon shugabancinsa na hada kowa da kowa da kuma kudurinsa na kawo ci gaba."
"Ina kira ga al’ummar jihar Taraba da su goyi bayansa wajen cika alkawuran da ya dauka."
- Kashim Shettima

Source: Facebook
Nentawe ya ji dadin shigowar Kefas APC
A halin da ake ciki kuma, shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwada, ya ce sauya shekar gwamnan babban karin karfi ne ga jam’iyyar da kuma jihar Taraba.
Yilwada ya bayyana matakin a matsayin wanda zai taimaka wajen bude dimbin damar tattalin arziki da ci gaba da ke jihar, yana mai tabbatar wa mambobin jam’iyyar adalci ga kowa.
"Shiga APC na daga cikin mafi kyawun shawarwarin da jihar Taraba ta dauka. Jihar na da albarkatu masu yawa, kuma wannan daidaito zai taimaka wajen sanya ta a sahun gaba na ci gaba.”
- Farfesa Nentawe Yilwatda
Ya kuma bukaci Gwamna Kefas da ya hada kan dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, yana mai tabbatar wa tsofaffi da sababbin mambobi samun dama iri daya a cikin APC.
Tinubu ya fadi su wanene shugabannin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jagororin jam'iyyar APC a matakin jihohi.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnonin da ke karkashin inuwar jam’iyyar APC su ne jagororin jam’iyyar a jihohinsu.
Kalaman shugaban kasar na zuwa ne yayin da wasu gwamnonin jam'iyyun adawa ke sauya sheka zuwa APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
