Gwamnatin Kano: Yadda Zaben Cike Gurbi Ya Tabbatar da Ikirarinmu a kan NNPP

Gwamnatin Kano: Yadda Zaben Cike Gurbi Ya Tabbatar da Ikirarinmu a kan NNPP

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ikirarin da ta yi a kan jam'iyyar da ta bari, NNPP ya kara fitowa sarari
  • Mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature D-Tofa ne ya bayyana haka yayin da ake shirin zaben cike gurbi a Kano
  • Sanusi Bature ya kara da cewa yayin da kowace jam'iyya ta mika sunaye dai-dai na kowane gurbi, NNPP ta mika uku

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnatin Kano ta bayyana cewa shirin zaben cike gurbi na ’yan majalisu a jihar ya tabbatar da ikirarin da ta yi na samun baraka mai girma a NNPP da ta bari.

Mai magana da yawun gwamna, Sanusi Bature D-Tofa ya ce yadda NNPP ta gabatar da ’yan takara uku daban-daban ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC).

Kara karanta wannan

Kano: NNPP ta dura a kan masu neman mataimakin Gwamna ya yi murabus

Gwamnatin Kano ta ce rikicin NNPP ya kara bayyana
Darakta janar kan yada labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: UGC

A sakon da ya wallafa a shafin Facebook, ya ce an muka sunayen ne domin cike gurbin ’yan Majalisar Dokokin Jiha a mazabun Ungogo da Municipal.

Gwamnatin Kano ta kare matsayarta kan NNPP

A cikin sakon, Sanusi Bature D-Tofa ya kara tabbatar da ikirarin da suka yi na cewa jam’iyyar na fama da rikicin cikin gida mai tsanani.

Gwamnatin ta ce wannan lamari ya bayyana karara gaban idon jama’a, tare da nuna barakar da ke ci gaba da girgiza jam’iyyar kafin zaben 2027.

A cewar bayanan da aka fitar, NNPP ta mika sunayen ’yan takara uku daban-daban ga hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC.

'Dan takara na farko ya fito ne daga bangaren Maikano Tarauni karkashin jagorancin Dungurawa a Kano.

Na biyu kuma ya fito daga bangaren Sanata Masa’udu Eljibrin Doguwa. Na uku kuwa ya fito daga bangaren Abiya, wanda daga bisani shi ne INEC ta amince da shi a hukumance.

Kara karanta wannan

"Ka nemi yafiya": Tsagin NNPP ya fadi yadda Kwankwaso ya kora Abba APC

Sanusi Bature ya ce sauran jam’iyyun siyasa da ke fafatawa sun gabatar da dan takara guda daya kacal a kowane gurbi.

Dalilan gwamnatin Kano na barin jam'iyyar NNPP

Gwamnatin Kano dai ta bayyana cewa daga cikin dalilan da suka kore ta daga NNPP akwai rikicin cikin gida da ya hana zaman lafya.

Gwamnan Kano da mutanensa sun bar NNPP ne saboda zargin rikicin cikin gida
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da ya bar NNPP Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sai dai bayan mika sunayen yan takara daban-daban ga INEC, kuma gwamnati ta kara cewa zargin da ta yi ba zargi ne kawai ba, ya tabbata.

Amma jama'a da dama sun yi martani kan lamarin, inda wasu suka yi tambayoyi, wasu kuma suka fadi ra’ayoyinsu kai tsaye.

Zaharaddeen Usman ya ce:

“Amma ta gabatar da dan takara guda daya ne kacal a zaben cike gurbi na Tsanyawa/Kunci da Bagwai, to me ya sa bangarori suka bayyana yanzu?”

Umar Garba ya ce:

“Ba shakka, idan aka duba tambarin jam’iyyar mai littattafai da sauran ’ya’yan itatuwa da kayan lambu, tun daga matakin kasa har zuwa mazabu, yanzu mun samu kwanciyar hankali kuma al’amura sun fito fili.”

Mashahud Abdullah Dawaki ya ce:

Kara karanta wannan

INEC ta jero jam'iyyun da za su fafata a zaben 'yan majalisun Kano

“Wannan rikicin cikin gida ya tabbatar da ikirarin cewa jam’iyyar na iya rugujewa kafin 2027.”

Shi ma Bashir A. H. Ashafalalah ya ce:

“Za ka yi ta bayani ka gaji, Malam Darakta Janar. Zan ba ka shawara kawai ka maida hankali kan aikinka na sauran watannin da suka rage. Rikici ko babu rikici a jam’iyyar, mutane ba wawaye ba ne, kuma za mu ga wanda zai yi dariyar karshe.”

Gwamnatin Kano ta fusata NNPP

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar NNPP ta yi Allah wadai da kalaman Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, na neman Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya ajiye aikinsa.

Wannan martani na NNPP na zuwa ne a wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar Kano, Ibrahim Karaye, ya fitar a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, 2026.

NNPP ta ce tsarin mulki na ƙasar nan har yanzu yana bai wa mataimakin gwamna cikakken iko da damar ci gaba da riƙe mukaminsa har zuwa ƙarshen wa’adin da aka zaɓe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng