Hadakar Atiku da Peter Obi Ta Yi Babban Kamu, Tsohon Gwamna Ya Shiga Tafiyar ADC
- Jam'iyyar hadaka, ADC ta yi kamun da ake hasashen zai kara mata karfi a jihar Kuros Ribas gabanin babban zaben shekarar 2027
- Tsohon gwamnan Kuros Riba, Donald Duke ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar ADC a hukumance yau Juma'a a Kalaba
- Shugabannin ADC sun yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kai da ita domin ceto kasar daga gurbataccen mulkin jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Cross River, Nigeria - Tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Donald Duke, ya fice daga jam’iyyar PDP, tare da komawa ADC yau Juma'a, 30 ga watan Janairu, 2026.
An yi wa Duke rajistar zama mamba na ADC a gunduma ta 5 da ke karamar hukumar birnin Kalaba, inda ya karbi katin jam'iyya a gaban dandazon magoya bayansa da ke ta shewa.

Source: Twitter
Tsohon gwamna ya shiga tafiyar ADC
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wannan ne karo na biyu da tsohon gwamnan yake barin jam’iyyar PDP.
Idan za a iya tunawa, a baya ya taba ficewa zuwa jam’iyyar SDP har ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin inuwarta, matakin da ya janyo ce-ce-ku-ce a lokacin.
A halin yanzu, tsohon gwamnan ya shiga ADC domin hada kai da manyan jagororin adawa irinsu tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi.
ADC ta ja hankalin mutanen Kuros Riba
A gefe guda kuma, shugabannin ADC na karamar hukumar Bakassi sun yi kira ga al’ummar jihar Kuros Riba da su hada kai su marawa jam’iyyar baya.
Sun yi wannan kiran ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya hada da mambobin kwamitin zartarwa na karamar hukumar, shugabannin gundumomi, da sakatarorin jam’iyyar na Bakassi.
Shugabannin sun bukaci ’yan Najeriya da su kwato kasar daga abin da suka kira mummunan mulki na jam’iyyar APC, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan
Buba Galadima ya kawar da NNPP, ya faɗi jam'iyyar da za ta kayar da Tinubu a 2027
Jam'iyyar ADC ta bude kofa ga 'yan Najeriya
A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba ranar Juma’a, jam’iyyar ADC ta ce:
“Muna gayyatar ’yan uwa da abokan arziki wadanda har yanzu ba su yanke shawara ba da su shigo ADC yau, domin jam’iyyar a shirye take ta kawo sauyi na gari a Najeriya.”

Source: Facebook
Sanarwar, wadda shugaban jam’iyyar na reshen Bakassi, Emmanuel Asuquo, da Sakatare, Eko Boco, suka sanya wa hannu, ta jaddada goyon bayan shugabancin ADC na kasa.
“Muna bayyana goyon bayanmu da amincewarmu ga shugabancin Sanata David Mark, ahugaban jam’iyya na kasa, da Ogbeni Rauf Aregbesola, sakataren jam’iyya na kasa.
"Muna mika mubaya’armu ga dukkan bangarorin jam’iyyar da aka sani a dukkan matakai yayin da muke kokarin gina jam’iyyar ADC mai karfi da hadin kai,” in ji sanarwar.
ADC ta kudiri aniyar ceto Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta koka kan salon mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya jefa jama'a cikin wahala.
Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa akwai hanyar da za a bi domin ganin an ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta a ciki.
Bolaji Abdullahi ya kuma soki halayen wasu mutane a cikin gwamnati, yana zarginsu da tafiyar da kasa da da yaren ’yan fashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

