Gaskiya Ta Fito kan Zargin Kwankwaso Ya Ci Amanar Ubangidansa a Jihar Kano

Gaskiya Ta Fito kan Zargin Kwankwaso Ya Ci Amanar Ubangidansa a Jihar Kano

  • Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayani kan zargin da ake cewa ya ci amaanar Sanata Hamisu Musa a siyasance
  • Wannan zargi ya sake tasowa ne yayin da dambarwar siyasar Kano musamman a tafiyar Kwankwasiyya ke kara kamari
  • Tun da Gwmana Abba Kabur Yusuf ya bar NNPP, aka fara musayar yawu tsakanin mabiyansa da wadanda ke tare da Kwankwaso

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na daga cikin fitattun ’yan siyasar da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu kan zargin cin amana ga wasu manyan abokan siyasar da suka taimaka musu a baya.

A halin yanzu, ana zargin Kwankwaso da cin amanar Sanata Hamisu Musa, wanda ake ganin ya taka rawar gani wajen gina tushen siyasarsa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya tuna bibiyar alkalan kotun koli da ya yi saboda Abba a zaben 2019

Kwankwaso.
Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a taron Kwankwasiyya a Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Wannan zargi ya sake daukar sabon salo ne a yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a Jihar Kano a baya-bayan nan, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kwankwaso ya ci amanar Hamisu Musa?

Sai dai Kwankwaso ya fito fili ya musanta wannan zargi, inda ya bayyana cewa abin da ya faru tsakaninsa da Sanata Hamisu Musa ba cin amana ba ne, illa sabanin fahimta da ya rikide zuwa babbar matsala.

A wani faifan bidiyo da tashar Siyasarmu TV ta wallafa a shafinta na Facebook, Kwankwaso ya ba da cikakken bayani kan yadda rikicin ya samo asali.

“Har yanzu bana jin dadin wannan lamari. Tare muke komai da Sanata, safe da dare muna tare. Wata rana mun rabu da niyyar za mu yi tafiya washe gari,” in ji Kwankwaso.

Abin da ya raba Kwankwaso da Sanata Hamisu

Ya ce a ranar da aka tsara tafiyar, Sanata Hamisu Musa ya zo gidansa da ke Abuja tare da iyalinsa, amma a lokacin yana zaune a falon gidansa tare da wasu mutane.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan cewa ya hada baki da Abba wajen shiga APC

“Na yi tunanin bari na gama ganawa da mutanen kafin mu fita tare. Aka tafi da iyalinsa sama wajen iyalina, amma aka tarar suna Sallah. Wannan ne ya sa ya dauka kamar wani shiri aka yi,” in ji shi.

Kwankwaso ya kara da cewa bayan ya kammala ganawarsa ya fito yana neman Sanata Hamisu Musa, sai aka shaida masa cewa ya riga ya tafi.

“Na kira shi a waya bai dauka ba. Aka sake kiran shi, sai ya ce sun yi nisa ba za su iya dawowa ba. Nan na rasa yadda zan yi,” in ji Kwankwaso.

Yadda Kwankwaso ya nemi sasanci

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa tun daga wannan lokaci mutane da dama, ciki har da Sarkin Dawaki, sun shiga tsakani domin a sasanta su, amma Sanata Hamisu Musa ya ki hakura.

Kwankwaso ya jaddada cewa ba da gangan ba ne abin da ya faru, kuma bai taba cin amanar Sanata Hamisu Musa ba tun lokacin da suke tare a siyasa.

Kwankwaso.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso yana hira da yan jarida Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya ce wannan lamari guda daya ne ya jawo sabanin da ke tsakaninsu, yana mai nuna alhini da nadama kan yadda alakar ta lalace duk da kokarin da ya yi na sasanci.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar da Kwankwaso ya yi fata Abba ya shiga maimakon hadewa da Ganduje a APC

Kwankwaso na ganin an ci amanarsa

A wani labarin, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da NNPP sun dauki sauya shekar Gwamnan Kano zuwa APC a matsayin cin amana.

Jam’iyyar NNPP ce ta bayyana hakan yayin da take kara nuna tsananin bacin ranta kan sauya shekar Gwamna Abba da mukarrabansa zuwa APC.

jam’iyyar ta ce ba ta da wani tsari na siyasa a jihar Kano kafin zaben 2023, amma duk da haka ta samu nasara kafa gwamnatin Abba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262