Bayan Shigar Abba Kabir, APC Ta Shirya Karbar Wani Gwamnan zuwa Cikinta

Bayan Shigar Abba Kabir, APC Ta Shirya Karbar Wani Gwamnan zuwa Cikinta

  • Ana ta shirye-shiryen karbar gwamnan jihar Taraba, Mista Agbu Kefas a hukumance zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Jam'iyyar APC ta sanya lokacin da za ta karbi gwamnan tare da sauya masu sauya sheka, bayan a baya an dage taron har sau biyu
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda za su halarci bikin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Taraba - Jam’iyyar APC mai mulki ta shirya karbar gwamnan jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, zuwa cikinta a 'yan kwanakin nan.

Jam'iyyar APC ta sanya ranar Asabar, 31 ga Janairu, 2026, domin karbar Gwamna Dr Agbu Kefas, a hukumance cikin jam’iyyar.

Za a karbi Gwamna Agbu Kefas a APC
Gwamna Agbu Kefas wajen rajista a jam'iyyar APC Hoto: Agbu Kefas
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce an shirya bikin sauya shekar ne a filin wasa na Jolly Nyame da ke Jalingo a ranar Asabar, 31 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sare gwiwoyin 'yan adawa, ya haska dalilan da za su sa APC lashe zabe a 2027

Gwamna Kefas ya gana da Shugaba Tinubu

Gwamna Kefas, wanda ya sauya sheka zuwa APC, ya riga ya kai ziyara ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaban APC na Kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

Daga bisani, gwamnan ya kira wani babban taron hadin gwiwa na masu ruwa da tsaki daga APC da PDP, irinsa na farko da aka taba gudanarwa a gidan gwamnati da ke Jalingo, inda manyan jiga-jigan jam’iyyun PDP da APC suka halarta.

Shettima zai karbi Kefas a jam'iyyar APC

Ana sa ran bikin sauya shekar zai ja hankalin magoya bayan jam’iyyar daga dukkan kananan hukumomi 16 na jihar, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da shugaban APC na kasa ne za su karbi Gwamna Kefas a hukumance tare da ‘yan majalisar dokokin jihar Taraba karkashin jagorancin shugabansu.

Sauran wadanda za a karba sun hada da, shugabannin kananan hukumomi 16 da kansilolinsu, mambobin majalisar zartarwa ta jihar, masu rike da mukaman siyasa, da kuma fitattun masu sauya sheka daga jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kara samun karbuwa a APC awanni 24 bayan ya shiga jam'iyyar

Ana kuma sa ran ‘yan majalisar tarayya daga jihar Taraba za su shiga wannan gagarumin sauya sheka zuwa APC.

Manyan bakin da za su halarci taron

Manyan baki da ake sa ran za su halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, gwamnonin da aka zaba a karkashin APC.

Sauran sun hada da ‘yan majalisar tarayya, da mambobin kwamitocin gudanarwa na jam’iyyar a matakin kasa, shiyya-shiyya da jiha.

Gwamna Agbu Kefas zai shiga APC a hukumance
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba zaune a ofis Hoto: Agbu Kefas
Source: Facebook

A baya an dage bikin sauya shekar sau biyu sakamakon matsalolin tsaro da ke faruwa a wasu sassan kasar.

Da yake tabbatar da wannan lamari, daraktan yada Labarai na APC a Taraba, Mista Aeron Atimas, ya ce taron zai zama wani babban ci gaba ga jam’iyyar a jihar.

A cewarsa, bikin zai kunshi dimbin masu sauya sheka da suka hada da kansiloli, shugabannin kananan hukumomi, ‘yan majalisar dokokin jihar da kuma ‘yan majalisar tarayya daga Taraba.

Gwamna Sule ya hango nasarar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya hango nasarar jam'iyyar APC a zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Bayan Abba, Kashim Shettima zai taso daga Abuja domin karbar gwamna zuwa APC

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da rike mulki a babban zaben 2027 da ake tunkara.

Abdullahi Sule ya nuna cewa 'yan adawa ba su da karfin da za su yi nasara a kan APC saboda suna fama da rikice-rikicen gida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng