Kwankwasiyya Ta Shiga Batun Neman Mataimakin Gwamna Kano Ya Yi Murabus

Kwankwasiyya Ta Shiga Batun Neman Mataimakin Gwamna Kano Ya Yi Murabus

  • An fara yin kiraye-kiraye ga mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam.Gwarzo, ya yi murabus daga kan mukaminsa
  • Kiraye-kirayen dai na zuwa ne bayan mataimakin gwamnan na Kano ya ki bin Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC
  • Kungiyar Kwankwasiyya ta fito ta yi martani ga masu neman mataimakin gwamnan ya yi murabus daga kan mukaminsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani kan kiraye-kirayen da ake yi na mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya yi murabus.

Kungiyar ta soki gwamnatin jihar Kano kan kiran Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya ajiye aikinsa, inda ta bayyana matakin a matsayin abin Allah-wadai.

An fara kiran mataimakin gwamnan Kano ya yi murabua
Aminu Abdulsalam Gwarzo, mataimakin gwamnan jihar Kano Hoto: Hon Aminu Abdulsalam Gwarzo
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, 29 ga watan Janairun 2026 wadda Hon. Habibu Saleh Mailemo, kakakin bangaren yada labarai na Kwankwasiyya ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Wasu kwamishinoni sun rikita gwamnatin Kano bayan komawar Abba APC? Gaskiya ta fito

Kwankwasiyya ta yi martani mai zafi

Martanin ya biyo bayan wasu kalamai da Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi, wadanda ke nuni da cewa ya kamata mataimakin gwamnan ya sauka daga mukaminsa.

Kungiyar ta ce kiran da ake yi wa Aminu Abdulsalam Gwarzo na ya yo murabus bai dace ba kuma na iya lalata daidaiton siyasa a jihar.

“Mun karanta cike da damuwa rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai da ke nuna cewa gwamnatin jihar Kano, ta hannun kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, ta bukaci mataimakin gwamna ya yi murabus."
"Muna kallon wannan kira a matsayin wanda bai da ce ba kuma abin takaici."

- Habibu Saleh Mailemo

Kwankwasiyya ta yi watsi da batun sauya mataimakin gwamnan Kano
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Amini Abdulsalam Gwarzo Hoto: Hon Aminu Abdulsalam Gwarzo
Source: Facebook

Matainmakin gwamna na da 'yanci

Kungiyar ta jaddada cewa an zabi mataimakin gwamnan ne a tikitin hadin gwiwa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, don haka yana da cikakken ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi kai tsaye daga hannun al’ummar jihar.

Kara karanta wannan

An nemi mataimakin gwamnan Kano da ya bi Kwankwaso ya yi murabus

“An zabi mataimakin gwamna ne a tikitin hadin gwiwa, kuma yana da halaccen iko na kundin tsarin mulki daga jama’ar jihar Kano. Mukaminsa ba ya karkashin ikon wani mutum guda."

- Habibu Salhe Mailemo

An ba gwamnatin Kano shawara

Kwankwasiyya ta kuma nuna cewa gwamnatin da ke ci a yanzu ta fito ne daga gagarumin tsarin siyasa da ya hada bangarori daban-daban, tana mai kira ga jami’an gwamnati da su fifita hadin kai da kwanciyar hankali a jihar.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta mayar da hankali kan mulki da yi wa al’umma hidima, maimakon rikice-rikicen cikin gida.

Kwankwasiyya ta kara da sake jaddada goyon bayanta ga mataimakin gwamnan, tare da kira ga ‘yan siyasa da su guji daukar matakan da za su iya haddasa tashin hankali a cikin gwamnati.

Mataimakin gwamnan Kano na tsaka mai wuya

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya ki bin Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam'iyyar APC.

Kin bin gwamnan ya jefa Aminu Abdulsalam Gwarzo cikin mawuyacin halin siyasa, inda ake hasashen rikici tsakanin bangarorin gwamnati da na jam’iyyun siyasa a jihar Kano.

Aminu Abdulsalam Gwarzo na iya fuskantar barazanar tsigewa daga majalisar dokoki domin raba shi da mukaminsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng