Wasu Kwamishinoni Sun Rikita Gwamnatin Kano bayan Komawar Abba APC? Gaskiya Ta Fito
- Rahotannin da ake yadawa cewa wasu kwamishinoni sun rikirkita gwamnatin jihar Kano, sun hana ta ayyuka sam ba gaskiya ba ne
- Kwamishinan yada labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce Gwamma Abba na da goyon bayan mambobin majalisar zartarwa ta jiha
- Ya jaddada cewa irin wadannan labarai na karya da kage ba za su dauke hankalin Gwamna Abba daga kokarin sauke nauyin da ke kansa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wasu kwamishinoni a Jihar Kano sun sake jaddada mubaya'a da biyayyarsu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinonin sun yi fatali da rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa akwai rabuwar kai a cikin majalisar zartarwa ta jihar Kano.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar yau Alhamis.
An samu sabani a Majalisar zartarwar Kano?
Ya bayyana irin wadannan rahotannin a matsayin na neman tada kura, ganganci, da kuma batar da mutane, yana mai nuni da cewa an tsara su ne domin karkatar da gaskiya.
Waiya ya jaddada cewa shugabanci yana tafiya ne bisa tsari, halacci, da ikon gudanarwa mai inganci, ba wai farfaganda ko hasashe ba, cewar rahoton Vanguard.
A cewarsa, kwamishinonin da ke jagorantar muhimman ma’aikatu wadanda ke aiwatar da manufofi, kula da kudaden gwamnati, da samar da ababen more rayuwa, suna tare da Abba Gida-gida.
Kwamishinoni sun yi mubaya'a ga Abba
Waiya ya lissafa ma’aikatun da kwamishinoninsu ke tare da Gwamna Abba, wanda suka hada da Ilimi, Lafiya, Ayyuka, Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Tsare-tsare da Kasafi, da Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida, da Shari’a.
Sauran sun kunshi ma'aikatun Kananan Hukumomi da Masarautu, Harkokin Noma, da Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Sufuri, Makamashi, Gidaje, Raya Karkara da Al'umma, da kuma bangaren Samar da Kayayyaki.
"Wadannan su ne tushen gwamnati kuma su ne cibiyoyin da ake yanke shawara tare da aiwatar da su. Duk abin da ya saba wa haka ko dai karya ce ko kuma yunkurin batar da jama’a,” in ji shi.
Gwamnatin Kano na aiki yadda ya kamata
Kwamared Waiya ya ce matukar wadannan ma'aikatu na aiki, harkokin shugabanci za su ci gaba da tafiya yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba a Kano.
Ya gargadi 'yan adawa da kada su jirkita kanun labaran siyasar da ke faruwa a Kano, inda ya ce duk da ƙungiyoyin siyasa na iya jan hankalin jama’a, babu abin da zai dakatar da tafiyar gwamnati.
Ya karkare da cewa gwamnatin Abba ba za ta bar wasu al’amuran siyasa su dauke mata hankali ko su raunana ta ba, inda ya jaddada cewa gwamnan yana ci gaba da gudanar da mulki yadda ya kamata.

Source: Facebook
Abba zai warware rikicin sarauta
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta bada tabbacin cewa rikicin masarautar Kano da ya dade yana daukar hankalin jama’a zai zo karshe cikin lumana nan ba da jimawa ba.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim.Waiya, ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Kano.
Waiya ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta riga ta shimfida tsare-tsare masu karfi domin tabbatar da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


