Bayan Gwamna Ya Fice daga PDP, Sanatan Filato Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar APC mai mulki a kasa ta sake samun gagarumin karfi a majalisar dattawa bayan sauya shekar Sanata Pam Dachungyang
- Sanata Dachungyang ya fice daga jam'iyyar ADP zuwa APC sakamakon rigingimun cikin gida da suka hana shi gudanar da ayyukansa
- Wannan sauya shekar na zuwa ne bayan tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar Simon Mwadkwon ya bar PDP zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An sake samun babban sauyin sheka a Majalisar Dattawan Najeriya a ranar Alhamis, inda Sanata Pam Mwadkon Dachungyang ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ADP.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar sauya shekar sanatan a babban zauren majalisar yayin zaman su na yau.

Source: Twitter
Sanatan Filato ya sauya sheka zuwa APC
Sanata Dachungyang ya bayyana cewa ya zaɓi komawa jam’iyyar APC ne domin samun kyakkyawan dandamali na yi wa al'ummar mazabarsa hidima yadda ya kamata, in ji rahoton The Nation.
A cikin wasiƙar tasa, Sanatan ya ambato cewa akwai rarrabuwar kai da tashe-tashen hankula a cikin gidan jam'iyyar ADP waɗanda suka kasa ƙarewa.
Ya bayyana cewa:
"Ficewata ta zama dole sakamakon rigingimun cikin gida a ADP waɗanda suka hana ni bayar da gudunmawar da ta dace ga al'ummar da nake wakilta."
Leadership ta rahoto dan majalisar ya ƙara da cewa ya gudanar da shawarwari na tsanaki tare da masu ruwa da tsaki da abokan siyasa kafin ya yanke wannan shawara ta komawa APC.
Karuwar karfin APC a Jihar Filato
Wannan mataki na Dachungyang yana zuwa ne makonni kaɗan bayan tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Simon Mwadkwon, ya bar PDP zuwa APC.
Mun rahoto cewa Simon Mwadkwon ya sanar da nasa sauyin shekar ne a lokacin da ya ziyarci dattawan jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Barkin Ladi dake Jihar Filato.
Mwadkwon ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar Sanatan Filato ta Arewa a ƙarkashin inuwar APC a zaɓen shekarar 2027 dake tafe, in ji rahoton The Cable.

Source: Facebook
Maraba da sababbin mambobin majals
Shugaban majalisar dattawan APC na Barkin Ladi, Solomon Bature, ya yi maraba da Simon Mwadkwon, inda ya bayyana cewa kofofin jam'iyyar a buɗe suke ga kowa.
Da sauya shekar Dachungyang, jam'iyyar APC ta cƙara yawan mambobinta a majalisar dattawa, sannan ta kuma kara karfi a siyasar jihar Filato.
Sanata Dachungyang dai ya jaddada cewa matakin nasa zai taimaka wajen tabbatar da jagoranci nagari da kuma samar da ci gaba mai ma'ana ga al'ummar gundumar sa ta Filato ta Arewa.
Gwamna ya bar PDP zuwa APC
Tun da fari, mun rahoto cewa, gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya koma jam’iyyar APC a hukumance bayan ficewarsa daga PDP.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar Plateau, Rufus Bature, ne ya mika masa katin zama ɗan jam’iyyar APC a ranar Juma’a, 2 ga watan Janairun 2026 a birnin Jos.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Mutfwang ya ce sauya shekar da ya yi zuwa APC na da nasaba da muradun jihar Plateau da ci gaban al'ummarsa.
Asali: Legit.ng

