"Ka nemi yafiya": Tsagin NNPP Ya Fadi Yadda Kwankwaso Ya Kora Abba APC
- Tsagin NNPP ya bayyana cewa ba da son ransa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da jam'iyya zuwa APC mai mulki ba
- Jam’iyyar ta zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da cin amanar wanda ya kafa NNPP, amma Abba bai ci amanarsa ba
- NNPP ta bayyana komawar Abba Yusuf APC a matsayin kariya daga tsoma baki a cikin harkokin mulki da Kwankwaso ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar NNPP ƙarƙashin Dr. Boniface Aniebonam ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bai rabu da Kwankwasiyya da NNPP don son ransa ba.
Tsagin jam'iyyar ya kara da cewa Abba ya bar NNPP ce saboda yunƙurin danniya da take-taken bautar da shi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke son yi.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Rabiu Kwankwaso ne ya ci amana, domin ya karya amincewar wanda ya kafa jam’iyyar NNPP, Dakta Aniebonam.
Tsagin NNPP ya goyi bayan Abba
A cewar tsagin jam’iyyar, duk wani yunƙuri da Abba Yusuf ya yi a matsayinsa na jagoran NNPP na sasanta rikicin cikin gida.
Wannan martani na NNPP ya biyo bayan kalaman Injiniya Buba Galadima dangane da ficewar Gwamna Abba Yusuf daga NNPP zuwa jam’iyyar APC.

Source: Facebook
A wata sanarwa da Mataimakin Shugaban NNPP na Yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Sani Danmasani, ya fitar, jam’iyyar ta shawarci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da mutanensa.
Ya yi kira ga iyalai da makusantan Kwankwaso da Inijiniya Buba Galadima da su shigo tsakani kafin lamarin ya rincabe baki daya.
Sanarwar ta ce ta yi nazari mai zurfi kan yanayin Buba Galadima yayin bayyanarsa a wani gidan talabijin, inda aka ga damuwa.
Tsagin NNPP ta ce komawar Abba Yusuf APC ta yi matuƙar shafar Kwankwaso da Galadima, lamarin da ya bayyana karara a cikin kalaman da suke furtawa cike da ɗaci da raɗaɗi.
Shawarar tsagin NNPP ga su Kwankwaso
Tsagin NNPP ta ce irin wannan damuwa na iya haifar da matsalar baƙin ciki mai tsanani da damuwa amatukar ba a ɗauki mataki a cikin gaggawa.
Jam’iyyar ta ce abin mamaki ne yadda ake zargin Abba Kabir Yusuf da cin amanar NNPP saboda ya koma APC, alhali Kwankwaso da Galadima su ne suka yi anfani da jam’iyyar ba tare da biyan komai ba.
Tsagin NNPP ya bayyana cewa matakin Abba Kabir Yusuf kariya ce ga kansa daga bautar zamani da tsoma bakin Kwankwaso cikin tafiyar da gwamnatin Kano.
Jam’iyyar ta shawarci Kwankwaso da magoya bayansa da su nemi shiriya da yafiyar Allah, tana mai jaddada cewa tasirin Kwankwaso a siyasar Kano ya ragu.
Kano: Za a kawo karshen dambarwar masarauta
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ta bai wa al’umma tabbacin cewa rikicin masarauta da ya dade yana daukar hankalin jama’a zai zo karshe cikin lumana.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Waiya, ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Kano kwanaki kadan bayan sauya shekar Gwamna.
Ibrahim Waiya ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta riga ta shimfida tsare-tsare masu karfi domin tabbatar da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa.
Asali: Legit.ng


