Gwamna Abba Ya Shiga APC da Kafar Dama, Ya Kara Samun Karbuwa daga Masoyan Tinubu
- Magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da mika sakon maraba ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano bayan ya koma APC
- Wata kungiyar tallata manufofin Shugaba Bola Tonubu (BAT-IG) ta bayyana farin ciki da sauya shekar gwamnan Kano zuwa jam'iyya mai mulki
- Ta ce karuwar da APC ke yi a sassa daban-daban na kasar nan alama ce ta yadda jama'a suka amince da salon mulkin shugaban kasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na ci gaba da samun sakonnin maraba da fatan alheri daga mambobin APC na sassa daban-daban na kasar nan kan shigarsa jam'iyya mai mulki.
Wata Kungiya mai tallata manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wato Bola Ahmed Tinubu Ideological Group (BAT-IG), ta yi mafaba da sauya shekar Abba Gida Gida zuwa APC.

Source: Facebook
Kungiyar BAT-IG ta yi maraba da Abba
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kungiyar BAT-IG ta bayyana matukar farin cikinta game da komawar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.
Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin babban abin karfafawa ga jam’iyyar da kuma yaduwarta a fadin kasa nan.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktar yada labarai ta kungiyar, Arabinrin Aderonke, ta aika wa manema labarai ciki har da jaridar Punch.
Idan ba ku manta ba, a ranar Litinin, 26 ga watan Janairu, 2026 Gwamna Abba da yan Majalisar dokokin Kano 22 da jami'an gwamnatinsa, suka koma APC a hukumance.
Gwamna Abba ya kara karfafa APC
Kakakin kungiyar BAT-IG ta bayyana cewa matakin da Gwamna Abba ya dauka na nuna karuwar amincewa da shugabanci, hangen nesa, da kuma tsarin tafiyar APC a karkashin Shugaba Bola Tinubu.
Har ila yau, kungiyar ta ce yadda mambobin jam'iyyar APC ke karuwa ta ko'ina a fadin kasar nan "manuniya ce karara ta yadda jama'a ke kara aminta da jagorancin Bola Tinubu."
Arabinrin Aderonke ta jaddada cewa wannan sauyin fasalin siyasa a jihar Kano zai karfafa jam'iyyar APC sosai gabanin babban zaben shekarar 2027.
"Ganin yadda bangarorin siyasa biyu da ke da karfin kuri’u a halin yanzu a Kano, jam’iyyar APC tana da kyakkyawar dama ta samun gagarumar nasara da dorewar kwanciyar hankali a fagen siyasa,” in ji ta.

Source: Facebook
Wannan sanarwa ta fito ne daga daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke tallata manufofin Shugaba Tinubu, wanda ke nuna cewa suna goyon bayan Gwamna Abba Gida-gida.
Murtala Garo ya yi maraba da Abba Kabir
A wani rahoton, kun ji cewa Murtala Sule Garo ya yi maraba da sauya shekar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin kasa.
Murtala Garo ya bayyana sauya shekar Gwamma Abba daga NNPP zuwa APC a matsayin mataki na samar da daidaiton siyasa da dorewar ci gaba a jihar Kano.
Tsohon dan takarar mataimakin gwamna na APC ya bayyana cewa a shirye yake ya bai wa Abba goyon bayan da ake bukata domin inganta rayuwar al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

