A Karshe, An Ji Matsayar Murtala Sule Garo kan Sauya Shekar Gwamna Abba zuwa APC
- Murtala Sule Garo ya yi maraba da sauya shekar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin kasa
- Garo, wanda ya yi takarar mataimakin gwamna a zaben 2023 karkashin inuwar APC, ya ce Abba ya dauki matakin da ya dace a siyasance
- Tsohon kwamishinan ya ce matakin da gwamna ya dauka ya nuna irin gogewarsa a fagen siyasa, wansa hakan zai amfanar da jihar Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - 'Dan takarar mataimakin gwamna na APC a zaben 2023, Murtala Sule Garo, ya yi maraba da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar.
Murtala Garo ya bayyana sauya shekar Gwamma Abba daga NNPP zuwa APC a matsayin mataki na samar da daidaiton siyasa da dorewar ci gaba a jihar Kano.

Source: Facebook
Garo, wanda tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu ne, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Talata, kamar yadda Punch ta rahoto.
Murtala Sule Garo ya yi maraba da Abba
Hon. Murtala Garo ya ce matakin gwamnan na komawa jam’iyya mai mulki ya nuna kwarewarsa a fagen siyasa da kuma hangen nesa, a daidai lokacin da Kano da ma kasa baki daya ke bukatar hadin kai da shugabanci na gari.
“Ina lale maraba da Mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zuwa cikin jam’iyyar APC."
"Wannan wani babban mataki ne abin a yaba a kokarinmu na neman daidaiton siyasa, shugabanci na bai-daya, da dorewar ci gaba a jihar Kano,” in ji sanarwar.
Garo ya jinjina wa Gwamna Abba Kabir
Murtala Sule Garo ya yaba da salon shugabancin Abba Gida-Gida, inda ya lura cewa natsuwarsa da jajircewarsa aun nuna cewa a shirye yake ya sanya muradun zaman lafiya da ci gaba gaba da na jam'iyya.
"Ta hanyar wannan mataki da ya dauka, mai girma gwamna ya nuna karfin ikon ketare rabuwar kawuna na jam’iyya domin tabbatar da zaman lafiya, ci gaba, da hadin kai,” in ji Garo.
Jigon a APC ya kara da cewa hadewar da gwamnan ya yi da jam’iyya mai mulki ya nuna karara cewa ya fahimci yanayin siyasa da tattalin arziki da jihar Kano da ma kasar baki daya ke fuskanta.
Murtala Garo zai hada kai da Abba
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa shigowar Abba cikin APC zai kara karfafa shirye-shiryen gyara jam’iyyar, sannan zai inganta hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kano da ta tarayya, cewar rahoton Daily Post

Source: Facebook
Garo ya sake jaddada biyayyarsa ga APC, inda ya yi alkawarin yin aiki tare da gwamnan da sauran masu ruwa da tsaki domin ciyar da Kano gaba, hadin kan siyasa, da manufofin da suka dace da jama'a a fadin jihar.
Wannan mataki na Murtala Garo ya janyo hankalin mutane da yawa, ganin yadda zaben 2023 ya kasance cike da hamayya tsakaninsa da Gwamna Abba.
Kwankwaso ya soki tafiyar Gwamna Abba
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna takaicinsa kan yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar jam'iyyar NNPP.
Sanata Kwankwaso ya ce sau da dama yana yin tunani a kan abin da ya faru tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana tambayar kansa ko shi ne ya yi laifi ko jam’iyya.
Ya ce duk da wannan nazari da yake yi, har yanzu bai samu amsar da za ta gamsar da shi ba, lamarin da ke ƙara nuna masa cewa sauya sheƙar gwamnan ta zo ne ba tare da dalili mai karfi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


