INEC Ta Jero Jam'iyyun da za Su Fafata a Zaben 'Yan Majalisun Kano

INEC Ta Jero Jam'iyyun da za Su Fafata a Zaben 'Yan Majalisun Kano

  • INEC ta tabbatar da jam’iyyu 10 da za su fafata a zaben cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano da za a yi ranar 21 ga Fabrairu
  • An karɓi takardun tsayawa takara daga jam’iyyu a Kano Municipal da Ungogo, yayin da ake ci gaba da lodawa ta yanar gizo
  • Hukumar ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen tabbatar da zaben a cikin nasara, tare da karin bayani a kan rikicin cikin NNPP

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoHukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa guda 10 za su shiga zaben cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugaban hukumar na Jihar Kano (REC), Ambasada Abdu Zango, yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Kano.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

INEC ta shirya zabe a Kano
Shugaban INEC na kasa, Joash Amupitan/Katin dangwala kuri'a a lokacin zabe Hoto: @SituationRoomNg/@inechq
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa za a gudanar da wannan zabe ne a ranar 21 ga Fabrairu, 2026.

Za a fafata a zaben Kano

Daily post ta ruwaito cewa Zango ya bayyana cewa, zuwa yanzu, INEC ta karɓi sunayen ‘yan takara daga jam’iyyun da aka yi wa rajista guda 10.

Shugaban hukumar zaben ya kara da cewa wadannan jam'iyyu ne za su fafata a kananan hukumomin Kano Municipal da Ungogo.

Ya ce jam’iyyun da suka mika takardunsu sun hada da APC, ADP, AAC, PRP, APGA, AA, LP da kuma NNPP.

Shugaban hukumar ya yi bayani cewa duk da cewa an mika sunayen ‘yan takara a matakin jiha, aikin lodawa da cikakken bayanan ‘yan takara na gudana ne a matakin hedikwatar jam’iyyu ta kasa, ta hanyar dandalin INEC na yanar gizo.

A kalamansa:

“Zuwa ranar karshe, mun karɓi sunayen ‘yan takara daga jam’iyyu 10. Ana ci gaba da lodawa, kuma INEC ta kasa ce kawai za ta tabbatar da adadin karshe bayan an kammala."

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya yi sababbin nade nade bayan ya koma APC

INEC ta kammala shirin zabe

Zango ya kara da cewa INEC ta tura jami’an sa ido daga hedikwatar kasa domin lura da zaben fitar da gwani na jam’iyyu a mazabun da abin ya shafa.

Dangane da rade-radin rikice-rikicen cikin gida a wasu jam’iyyu, musamman NNPP, Shugaban ya jaddada cewa INEC ba ta samu wata umarnin kotu kan batun ba.

Jam'iyyu 10 za su fafata a zaben Kano
Taswirar jihar Kano inda za a fafata zaben cike gurbi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Haka kuma ya ce a a samu wata sanarwa da za ta shafi tantance shugabancin jam’iyya ko zaben fitar da gwani ba.

A cewarsa:

“Ba mu da labarin wata takardar kotu. Ayyukan INEC suna tafiya ne bisa doka da rahotannin fitar da gwani da aka sa ido a kansu."

Zango ya tabbatar wa jama’a cewa shirye-shiryen hukumar sun yi nisa matuka, inda ya ce zaben cike gurbin zai gudana a mazabu biyu na jiha a Kano Municipal da Ungogo.

Ya ara da cewa kusan mutane rijista 535,000 sun yi rajista, kuma za a yi zaben a rumfunan zabe sama da 1,000.

Kara karanta wannan

Awanni da shigar Abba APC, kotu ta garkame wasu manyan ma'aikatan gwamnatin Kano

Ya bukaci masu kada kuri’a da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin amfani da ‘yancinsu, yana mai tabbatar da cewa an tanadi isassun ma’aikata da kayan aiki domin sahihin zabe mai adalci.

INEC ta dawo da rajistar zabe

A baya, mun wallafa cewa hukumar INEC ta sanar da dawo da aikin rajistar masu jefa ƙuri’a a duk faɗin Najeriya, lamarin da ke nuna fara zagaye na biyu na shirin rajistar.

Dawowar aikin na zuwa ne bayan da aka kammala zagaye na farko, wanda aka rufe shi a hukumance a ranar 10 ga Disamba, 2025, kamar yadda INEC ta sanar tun da farko.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, INEC ta bayyana cewa ta yi amfani da tazarar da ke tsakanin zagaye na farko da na biyu wajen aiwatar da wasu muhimman ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng