Buba Galadima Ya Yi Tone Tone kan Abba, Ya Fadi Alherin da Buhari Ya Masu

Buba Galadima Ya Yi Tone Tone kan Abba, Ya Fadi Alherin da Buhari Ya Masu

  • Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana sauya sheƙar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a matsayin mafi muni a tarihin duniya
  • Buba Galadima ya bayyana cewa ficewar Abba daga NNPP zuwa APC an yi ta ne bisa muradin kai, ba don jama’ar Kano ko zaman lafiya ba
  • Ya yi bayani game da abin da Muhammadu Buhari ya fada da irin rawar da suka taka kafin Abba ya zama gwamna bayan dogon lokaci a kotu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi kakkausar suka kan sauya sheƙar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC, inda ya kira lamarin a matsayin “cin amana mafi muni” da ya taɓa faruwa.

A cewarsa, ficewar gwamnan daga NNPP a ranar 23 ga watan Janairun 2026, da kuma komawarsa APC a hukumance a ranar Litinin da ta biyo baya, lamari ne da ya girgiza jam’iyyar da magoya bayanta.

Kara karanta wannan

'Tun farkon mulki ne': An fadi lokacin da Abba ya fara bijirewa Kwankwaso a Kano

Rabiu Musa Kwankwaso da Buba Galadima
Gwamna Abba Kabir da Kwankwaso a hagu, Buba Galadima a dama. Hoto: Kwankwasiyya Reporters| Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Buba Galadima a bayyana hakan ne yayin da aka yi hira da shi a shirin Prime Time na tashar Arise Television, inda ya ce abin da Abba Kabir Yusuf ya yi muni.

'Abba ya ci amana,' Buba Galadima

Da yake martani kan sauya sheƙar, Buba Galadima ya ce ya kamata a rubuta abin da Abba Kabir Yusuf ya yi a kundin Guinness World Records, tare da ayyana 23 ga watan Janairu a matsayin “Ranar Cin Amana ta Duniya.”

Ya ce ficewar gwamnan ba ta da wata alaƙa da muradin al’ummar Kano, illa muradin kansa. A cewarsa:

“Abba Kabir Yusuf ya yi wannan ne domin amfanin kansa, ba don jama’ar Kano ba, ba don zaman lafiya ba.”

Buba Galadima ya ƙara da cewa shekarunsa sun haura 75, kuma duk da cewa ba ya yawan zubar da hawaye, wannan lamari ya taɓa shi matuƙa fiye da misali.

Alakanta sauya sheƙar Abba da tarihi

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya magantu kan dalilan da Abba ya fada masa yayin shiga APC

A wata magana mai ɗaukar hankali, Buba Galadima ya kwatanta abin da Abba Kabir Yusuf ya yi da manyan cin amana a tarihin bil’adama.

The Sun ta rahoto ya ce:

“Wannan cin amana ita ce ta uku a tarihin ɗan Adam; na farko shi ne abin da Yahudawa suka yi wa Annabi Isa, ta biyu kuma abin da Brutus ya yi wa Caesar.”

Ya jaddada cewa ba zai iya karɓar hujjar da ke nuna cewa ficewar ta amfani jama’ar Kano ba, yana mai cewa duk abin da gwamnan ya yi ya ta’allaka ne kan “muradin kai, muradin kai, muradin kai.”

Rawar Buhari da kotuna a nasarar Abba

Buba Galadima ya kuma yi ikirarin cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf bayan doguwar shari’a.

Ya ce:

“Mutumin da aka taɓa kwace mana nasara a lokacinsa a 2019 ya tsaya tsayin daka daga baya ya ce, ‘Wannan yaro ya ci zaɓe, a ba shi nasararsa.’”

A ƙarshe, Galadima ya zargi gwamnan da watsi da aƙidu da ka’idojin siyasar da suka ɗaura shi kan mulki, yana mai cewa wannan mataki zai ci gaba da ɗaukar hankali a siyasar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan cewa ya hada baki da Abba wajen shiga APC

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
Marigayi Muhammdu Buhari a fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Maganar sulhun Ganduje da Kwankwaso

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan alakarsa da Rabiu Kwankwaso.

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa kofar sulhu tsakaninsa da Kwankwaso a bude ta ke lura da cewa dukkansu Musulmai ne.

Ganduje da ya taba zama mataimakin Kwankwaso, ya yi wannar maganar ne bayan Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC daga NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng