Kwankwaso Ya Fadi Yadda Yake Kallon ’Yan Kwankwasiyya da Suke tare da Abba Kabir

Kwankwaso Ya Fadi Yadda Yake Kallon ’Yan Kwankwasiyya da Suke tare da Abba Kabir

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana takaicinsa kan sauya shekar Gwamna Abba Kabir, yana cewa abin ya zo musu a matsayin babban abin mamaki
  • Kwankwaso ya ce duk wanda ya bi Abba zuwa APC, ko da jar hularsa, ba ya cikin Kwankwasiyya, ana kallonsa a matsayin dan Gandujiyya
  • Jagoran Kwankwasiyya ya kalubalanci Ganduje, yana cewa daga hannun Abba Kabir Yusuf alama ce ta faduwa a zabe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sake magana game da sauya shekar Gwamna Abba Kabir zuwa APC.

Kwankwaso ya nuna takaici kan abin da ya faru wanda ya ce abin mamaki ne saboda ba su yi tsammani ba ko kadan.

Kwankwaso ya nuna takaici kan butulcin Abba Kabir
Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso ya ce ba su tare da 'munafukai'

Jagoran Kwankwasiyya ya bayyana haka ne yayin hira da BBC Hausa a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafin Facebook a yau Laraba 28 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

'Barazanar da Abba Kabir zai fuskanta daga Kwankwaso a 2027 bayan bijire masa'

A cikin bidiyon, Kwankwaso ya ce duk wadanda suka bi Abba amma suna cewa suna Kwankwasiyya ba su tare da su.

Da aka tambaye shi ko ya yake kallon wadanda suka bi Abba Kabir Yusuf amma sun ce ba su bar Kwankwasiyya ba, ko zai amince da haka?, Kwankwaso ya ce:

"Ba magana ce ta amincewa ba, magana ce ta an riga an gina haske, an gina duhu a Kano, idan mutum yana haske ya koma duhu ya ce shi haske ne, ai ba su haduwa.
"Akidarmu daban take, tsarinmu daban yake, shiyasa mutane wasu suke sonmu, wasu ba su sonmu.
"Idan za ka yi Kwankwasiyya wa ya ce ka fita daga cikinta, ka tsaya ka yi Kwankwasiyyar mana a inda take."
Kwankwaso ya dura kan wadanda suka ci amanarsa
Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir na Kano. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

Kwankwaso ya dura kan yan Gandujiyya

Kwankwaso ya ce duk wanda ya saka jar hula bayan ya bar Kwankwasiyya to bai tare da su kuma suna ganinsa dan Gandujiyya ne kawai.

Ya kuma kalubalanci Abdullahi Ganduje bayan daga hannun Abba Kabir da cewa wannan shi ke nuna alamar sun fadi kasa a zabe.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar da Kwankwaso ya yi fata Abba ya shiga maimakon hadewa da Ganduje a APC

"Domin haka duk wanda ya fita ko ya saka jar hula, ya zama dan Gandujiyya ka narke haka za mu ganka, haka duk jama'a za su ganka kamar yadda muke ganin Ganduje.
"Kuma musamman yadda na ga an nuna min a takarda Ganduje ya daga masa hannu, mu a wurinmu wannan daga hannu da ya yi ya fadi zabe."

- Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso ya ce da Ganduje yana da hannun dagawa da ya daga a 2019 da kuma 2023 saboda jama'ar Kano ba su son wannan tsarin.

Fasto ya gargadi Abba bayan barin Kwankwaso

Mun ba ku labarin cewa Fasto Elijah Ayodele ya tsoma baki game da ficewar Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Limamin ya gargadi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, cewa burinsa na wa’adi na biyu na fuskantar barazana mai tsanani.

Ayodele ya yi hasashen rikicin siyasa a Kano, tare da gargadin Tinubu kada ya yarda da duk masu sauya sheka zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.