Gwamna Abba Ya Kara Samun Karbuwa a APC Awanni 24 bayan Ya Shiga Jam'iyyar

Gwamna Abba Ya Kara Samun Karbuwa a APC Awanni 24 bayan Ya Shiga Jam'iyyar

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na ci gaban da samun karbuwa a wurin manyan jiga-jigan APC musamman a Arewacin Najeriya
  • APC ta shiyyar Arewa maso Yamma ta yabawa Abba Gida-Gida bisa matakin da ya dauka, tana mai cewa Kano za ta samu karin ayyukan ci gaba
  • Shugaban APC na Arewa maso Yamma, Hon. Garba Datti Muhammad ya ce Abba ya yi abin da ya dace domin ci gaba Kano da al'ummarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jam’iyyar APC ta shiyyar Arewa maso Yamma ta bayyana matakin da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauka komawa jam’iyyar a matsayin mafi hikima da ya taba dauka tun bayan shigarsa fagen siyasa.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, shugaban APC na shiyyar kuma tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Garba Datti Muhammad, ya ce sauya shekar Abba ta nuna jajircewarsa ga shugabanci na gari.

Kara karanta wannan

Bayan shigan Abba APC, NNPP ta yi maganar butulci, shirin kifar da shi a 2027

Gwamna Abba Kabir.
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Ya ce sauya shekar Abba Gida-Gida daga NNPP zuwa APC ta kara karfafa jam'iyya mai mulkin a fadin Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

APC ta kara jinjinawa Gwamna Abba

Ya bayyana cewa shawarar da Gwamna Abba ya yanke tana nuna daidaiton ra'ayinsa da manufofin APC na kawo ci gaba da kuma yadda jam'iyyar ke kara fadada a sassan kasar nan.

“Muna maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf da dukkan zuciyarmu zuwa APC. Shawarar da ya yanke na mara wa manufar ci gaba baya shaida ce ta tasirin ajendar 'Renewed Hope' ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu," in ji Muhammad.

Hon. Garba Datti ya bayyana cewa ta hanyar komawa APC, Gwamna Abba ya dauki mataki mai kyau a rayuwarsa ta siyasa, inda ya zo da dubun-dubatar magoya bayansa da masu masa biyayya.

Matakin Abba zai kawo ci gaba a Kano

Ya ce gwamnan ya bar bangaren hamayya ya dawo cikin "tsarin siyasar kasa," wanda hakan zai kawo karin ci gaba ga jihar Kano, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

A cewar tsohon dan Majalisar, wannan mataki ya sake sanya Kano a cikin taswirar siyasa mai ra'ayin ci gaba wadda aka san ta da ita shekaru da dama da suka gabata.

Hon. Datti ya lura cewa yanzu lokaci ne da APC za ta kafa karfafa kanta, duba da yadda gwamnoni, 'yan majalisar tarayya da na jiha, da sauran jiga-jigan siyasa ke kwararowa cikin jam’iyya mai mulki.

Sanarwar ta kammala da cewa:

"Za mu ci gaba da kara karfi yayin da muke tunkarar babban zaben 2027. Ga mu a APC, muna maraba da kowa."
Jam'iyyar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

NNPP ta zargi Abba da cin amana

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar NNPP ta kara nuna tsananin bacin ranta kan sauya shekar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.

NNPP ta bayyana cewa tsohon dan takararta na shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dauki lamarin matsayin cin amana.

Da aka tambaye shi ko Sanata Kwankwaso yana jin an yaudare shi, Johnson ya ce wannan cin amana ya wuce kan jagoran jam’iyyar kawai, har ma da al’ummar jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262