Tsaka Mai Wuya da Mataimakin Gwamnan Kano ke ciki bayan Abba Ya Shiga APC

Tsaka Mai Wuya da Mataimakin Gwamnan Kano ke ciki bayan Abba Ya Shiga APC

  • Gwamnan Kano Abba Yusuf ya koma APC wanda ya jawo hasashe kan makomar mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo
  • Kwamred Gwarzo ya ƙi bin sa jam'iyyar APC da ake ganin yana tare da Kwankwasiyya lamarin da ya jefa siyasar jihar cikin rikici
  • Tsohon mataimakin gwamnan Neja, Ahmed Ketso, ya ce ƙin sauya sheƙa na iya kai Gwarzo ga barazanar tsige shi a Majalisar Dokoki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Bayan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC, mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ƙi bin sa.

Wannan mataki ya jefa Gwarzo cikin mawuyacin halin siyasa, inda ake hasashen rikici tsakanin bangarorin gwamnati da na jam’iyyun siyasa a jihar Kano.

Mataimakin Abba Kabir na iya fuskantar barazanar tsigewa
Gwamna Abba Kabir da mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Twitter

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Niger, Ahmed Mohammed Ketso ne bayyana haka yayin zantawa da jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Abba ya fitar da 'yan takarar APC da za su kalubalanci Kwankwaso a zabe

An san Gwarzo a matsayin jajirtaccen 'dan tafiyar Kwankwasiyya, wadda ke da karfi a siyasar Kano.

Ficewar Abba zuwa APC ya rikita siyasar Kano

Gwamna Yusuf ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC tare da ’yan majalisar jiha 22 da sauran manyan ’yan siyasa.

Majalisar Dokokin Kano ta sanar da cewa mambobinta 22 sun koma APC, lamarin da ya ba APC rinjaye a majalisar.

Kafin sauya sheƙar, NNPP na da ’yan majalisa 24, APC na da 14, amma biyu daga cikin 'yan majalisan NNPP sun rasu.

Abba Kabir ya sauya sheka ba tare da mataimakinsa ba
Gwamna Abba Kabir yayin taron majalisar zartarwa. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Facebook

Matsalar da Abdulsalam Gwarzo ka iya fuskanta

Ketso ya bayyana cewa Gwarzo na iya fuskantar barazanar tsigewa daga majalisar dokoki domin raba shi da mukaminsa.

'Dan siyasar ya ce ko da gwamna da mataimakinsa sun yi ƙoƙarin fahimtar juna, masu ba su shawara za su iya haddasa rashin yarda tsakaninsu.

Ya ce Majalisar Dokokin Jihar Kano na iya taka rawa wajen tsige mataimakin gwamnan.

Ya ce:

“Sun zo ne da tikitin hadin gwiwa, amma Majalisar Dokoki na iya ɗaukar mataki idan rikici ya ƙara tsananta.”

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

Ketso ya ƙara da cewa idan shi ne a irin wannan matsayi, zai fi son yin murabus maimakon fuskantar tsige wa.

Duk da haka, ya kawo misalin Jihar Sokoto inda gwamna da mataimakinsa suka gudanar da mulki duk da bambancin siyasa.

Tarihin siyasar Gwarzo ya haɗa da zama mataimakin gwamna, kwamishina, da shugaban karamar hukuma a lokuta daban-daban.

Gargadin kungiyar manyan Arewa kan siyasar Kano

Kungiyar ACF ta gargadi ’yan siyasa da su guji daukar matakan da za su haddasa rikici a jihar Kano.

ACF ta ce tsige mataimakin gwamna zai zama abin bakin ciki ga dimokuradiyya kuma zai iya haddasa tarzoma.

Ya ce Kano jiha ce mai tasiri a siyasa, kuma rashin hankali zai iya haddasa babbar matsala.

Abba ya fitar da 'yan takarar APC

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zaɓi ’yan takarar APC domin cike gurbin kujerun ’yan majalisar jiha biyu da suka rasu.

Rahotanni sun nuna cewa Hon Alhajiji PA Kankarofi zai tsaya takara a birnin Kano, yayin da Hon Musayyib Kawu Ungogo zai fafata a mazabar Ungogo.

Hakan na zuwa ne bayan Rabiu Kwankwaso ya tsayar da ’ya’yan marigayan ’yan majalisar domin tsayawa takara a zaɓen cike gurbin da za a yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.