Tazarcen Shugaba Tinubu a 2027 Ya Samu Gagarumin Tagomashi daga Arewa

Tazarcen Shugaba Tinubu a 2027 Ya Samu Gagarumin Tagomashi daga Arewa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu tagomashi kan zaben shekarar 2027 duk da bai bayyana cewa zai tsaya takara ba
  • Wata kungiyar matasan Arewa ta nuna goyon bayanta ga tazarcen shugaban kasar a zaben 2027 da ake tunkara
  • Kungiyar ta bayyana shirin da ta yi domin shugaban kasar kan batun sake neman kujerar shugabancin Najeriya a 2027

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar shugabannin matasan Arewa (NNYLF) ta goyi bayan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Kungiyar matasan ta bayyana cewa ta tara N200m domin sayen fom ɗin tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar don tazarcen Shugaba Tinubu gabanin zaben 2027.

Kungiyar matasan Arewa ta goyi bayan tazarcen Shugaba Tinubu
Mai girma Bola Ahmed Tinubu, shugaban kasar Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce kungiyar ta bayyana hakan ne ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 a wani babban taron shugabannin matasa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Sai Tinubu: 'Dan Atiku ya sha alwashi, za a hadu da shi a kada mahaifinsa a 2027

Kungiyar matasan Arewa ta goyi bayan Tinubu

Ta kuma bayyana goyon bayanta ga Shugaba Tinubu domin ya yi wa’adi na biyu, tana mai nuna bukatar ci gaba da manufofi, ƙarfafa sauye-sauyen da aka fara da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa ga ƙasa.

A yayin taron, shugabannin kungiyar sun miƙa cak ɗin Naira miliyan 200 ga shugaban kungiyoyin goyon bayan Tinubu, Dr. Umar Tanko Yakasai.

A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron, wadda shugaban kungiyar na kasa, Murtala Gamji, da daraktan Ayyuka, Agbana John, suka sanya wa hannu, kungiyar ta sha alwashin ci gaba da wayar da kan matasan Arewa cikin lumana.

Za a wayar da kan matasa

Ta ce za ta wayar da kan matasan ne bisa batutuwan da suka shafi manufofi, tare da mai da hankali kan shiga harkokin dimokuraɗiyya, haɗin kan kasa.

Sanarwar ta ce an kira taron ne domin tantance ci gaban kasa a karkashin (Renewed Hope Agenda), kara shigar matasa cikin harkokin mulki, bayyana goyon baya ga Shugaba Tinubu domin wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan

Kwanaki kadan da dawowa, Shugaba Tinubu ya sake barin Najeriya

Har ila yau, kungiyar ta yi alƙawarin karfafa zaman lafiya da ɗabi’ar siyasa mai nagarta, tare da yin watsi da duk wani nau’i na tashin hankali, yaɗa ƙarya da kuma labaran da ke rarraba al’umma.

Kungiya za ta sayawa Tinubu fom

Jaridar The Guardian ta ce da yake zantawa da ’yan jarida bayan taron, Murtala Gamji ya ce Shugaba Tinubu ya yi aiki yadda ya kamata kuma ya cancanci sake samun wa’adi na biyu.

Tinubu ya samu goyon baya kan tazarcen 2027
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook
“Tare da goyon bayan kwamitocin amintattunmu da manyan masu tallafa mana, da dama daga cikinsu suna nan a wannan wuri, da kuma goyon bayan shugaban kungiyar goyon bayan Tinubu, wanda shi ma ɗan Arewa ne, mun yanke shawarar tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Naira miliyan 200."
“Idan lokacin sayar da fom ɗin tsayawa takara ya yi, za mu saya wa shugaban kasa fom ɗin domin ya sake tsayawa wa’adi na biyu, saboda muna da yakini kan haɗin kan Najeriya.”
“Muna kuma girmama yarjejeniyar da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu cewa Kudancin Najeriya ya kammala wa’adin shekaru takwas kafin mulki ya koma Arewa."

- Murtala Gamji

Kara karanta wannan

Dogara: Kiristan da aka ce zai maye Shettima a 2027 ya fito ya yi magana

Legit Hausa ba ta tabbacin cewa an yi wata yarjejeniya tsakanin marigayi Muhammadu Buhari da Bola Tinubu na ganin mulki ya yi shekaru takwas a yankin Kudu.

'Dan Atiku ya goyi bayan tazarcen Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Abubakar Atiku Abubakar wanda yake da ne a wajen Atiku Abubakar ya goyi bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

'Dan na tsohon mataimakin shugaban kasar, ya bayyana cewa babu wata jam’iyyar siyasa ko haɗakar jam’iyyu da za su iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu komawa fadar Aso Rock.

Abba Atiku ya jaddada cewa Shugaba Tinubu na tafiyar da mulki bisa adalci da cancanta, ba tare da nuna bambancin kabila, addini ko yanki ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng