An Zo Wajen: Gwamna Zulum Ya Tsage Gaskiya kan Wanda Zai Gaje Shi a 2027
- Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Borno, sun gudanar da muhimmin taro a birnin Maiduguri, babban birnin jihar
- Gwamnan jihar Borno ya yi tsokaci a wurin taron kan wanda zai gaje shi bayan ya kammalaa wa'adinsa a shekarar 2027
- Hakazalika, Gwamna Zulum ya kuma kafa kwamitin da zai jagoranci aikin sasanta 'ya'yan jam'iyyyar APC a jihar Borno
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi magana kan wanda zai gaje shi a zaben shekarar 2027.
Gwamna Babagana Zulum ya bayyana cewa bai san wanda zai gaje shi ba bayan karewar wa’adinsa a watan Mayun 2027.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Janairun 2026 yayin wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC
Masu ruwa da tsaki na APC sun yi taro
An gudanar da muhimmin taron ne a babban dakin taro na fadar gwamnatin jihar Borno da ke birnin Maiduguri, jaridar Leadership ta kawo labarin.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta maida hankali ne wajen ƙarfafa tsaro da kuma samar da ci gaban da al’ummar jihar ke buƙata.
Da yake jawabi ga shugabannin jam’iyya, zaɓaɓɓun jami’ai da mambobi, Zulum ya sake nanata matsayinsa na tabbatar da adalci, gaskiya da daidaito a tsarin zaɓen shugabannin jam’iyya a yayin zabubbukan da ke tafe.
Gwamna Zulum ya kuma yi watsi da rade-radin da ke cewa yana da tasiri wajen tsara tikitin jam’iyyar a nan gaba.
Wane ne zai gaji Gwamna Babagana Zulum?
Ya bayyana a fili cewa bai tsayar da wani ɗan takara ba, ko don muƙaman jam’iyya ko kuma kowane mukamin zaɓe ba.
“Ba ni da ɗan takara a kowanne matsayi, kuma ban san wanda zai gaje ni ba. Na damƙa zaɓin shugabanni ga Allah Maɗaukakin Sarki, bisa ga tsarin dimokiraɗiyya da muradin mambobin jam’iyya da al’ummar jihar Borno."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Zulum ya kafa kwamitoci kan ayyukan APC
Gwamnan ya kuma kafa kwamitoci biyu domin kara inganta rajistar APC ta yanar gizo da kuma sasanta mambobin jam’iyyar.
Kwamitin mai mutum 10 zai kasance karkashin jagorancin tsohon jakadan Najeriya a kasar China, Baba Ahmed Jidda, kuma ya kunshi mambobi daga mazabun sanatoci uku na jihar.
Ambasada Baba Ahmed Jidda mai shekaru fiye da 70 a duniya ya rike mukamai da dama a karamar hukumarsa ta Marte, jihar Borno da kuma gwamnatin tarayya.
Jiga-jigan APC sun halarci taro
Taron ya samu halartar Mukaddashin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur; tsohon Gwamnan jihar Borno, Maina Ma’aji Lawan; Mataimakin shugaban APC na kasa, Ali Bukar Dalori; Shugaban APC na Jihar Borno, Bello Ayuba.

Source: Facebook
Sauran mahalarta taron sun hada da tsofaffin Mataimakan gwamnan jihar uku da suka haɗa da Ali Abubakar Jatau, Adamu Shettim Dibal da Usman Mamman Durkwa.
Hakazalika, babban mai tsawatarwa na Majalisar dattawa, Mohammed Tahir Monguno; Sanata Kaka Shehu Lawan; da ’yan majalisar wakilai 10, ciki har da Midala Balami wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, sun halarci taron.
Gwamna Abba ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a hukumance bayan ficewa daga NNPP.
Gwamna Abba ya shiga APC ne a gaban tsohon shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Hakazalika, Gwamna Abba ya jaddada cewa dalilin komawarsa APC shi ne domin samar da kyakkyawar dangantaka da hadin kai tsakanin Kano da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

