Bayan Dan Kwankwaso, Wasu Karin Kwamishinoni Sun Yi Murabus daga Gwamnatin Abba
- Wasu daga cikin kwamishinonin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano na ci gaba da ajiye mukamansu bayan komawarsa jam'iyyar APC
- Gwamna Abba Kabir Yusuf dai ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026 bayan ya fice daga NNPP
- Kwamishinan ayyuka na musamman, Nasiru Sule Garo, na daga cikin kwamishinonin da suka aika da takardar murabus dinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Air Vice Marshal Ibrahim Umaru (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa na Kwamishinan tsaron cikin gida da harkoki na musamman na jihar Kano.
An bayyana murabus ɗin Ibrahim Umaru ne ta wata wasika da ya rubuta zuwa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hannun sakataren gwamnatin jiha, wadda ke ɗauke da kwanan wata 26 ga Janairu, 2026.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce a cikin wasikar, tsohon jami’in rundunar sojin saman ya nuna godiyarsa ga gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa.
Kwamishina ya bar gwamnatin Abba
Ibrahim Umaru ya tuno da yadda aka fara naɗa shi a matsayin shugaban sashen ayyuka na musamman a watan Yunin 2023, kafin daga bisani a kara masa girma zuwa matsayin kwamishina.
Ya bayyana cewa shawarar barin mukamin ta biyo bayan sauye-sauyen siyasa na baya-bayan nan, yana mai cewa ya ga hakan ya fi dacewa da muradin jihar da kuma gwamnatin da yake yi wa hidima.
“Biyo bayan abin da ya faru a baya-bayan nan, na yanke shawarar cewa ya fi dacewa da muradin jihar da gwamnatin cewa na janye daga wannan mukami. Ko da yake shawarar tana da wahala, amma an ɗauke ta ne bayan yin dogon nazari."
- Ibrahim Umaru
Ibrahim Umaru ya ce hidimarsa a gwamnati ta kasance bisa turbar ka’idojin tafiyar Kwankwasiyya, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wadda ya ce tana jaddada adalci, ladabi da yi wa al’umma hidima.
Nasiru Sule Garo ya bar gwamnatin Abba
A gefe guda kuma, kwamishinan ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo, shi ma ya yi murabus daga mukaminsa, jaridar Daily Trust ta dauko labarin.
Nasiru Sule Garo ya sanar da murabus ɗinsa ne ta wata wasiƙa da ya rubuta zuwa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hannun sakataren gwamnatin jihar, mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Janairun 2026.
A cikin wasiƙar, tsohon kwamishinan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan yin tunani mai zurfi, yana mai bayyana cewa yi wa al’ummar jihar Kano hidima ya kasance abin alfahari a gare shi.

Source: Facebook
“Ina matuƙar godiya bisa amincewa da goyon bayan da aka nuna mini a lokacin da nake kan mukami."
"Yi wa al’ummar jihar Kano hidima ya kasance abin alfahari a gare ni, kuma ina godiya da damar da aka ba ni na ba da gudunmawa wajen cigaban jiharmu da aiki tare da abokan aiki masu kwazo."
- Nasiru Sule Garo
Ya shirya mika mulki
Nasiru Sule Garo ya ce ya shirya tabbatar da mika mulki cikin kwanciyar hankali, yana mai cewa zai kasance a shirye don taimakawa duk wata bukatar mika ayyuka yadda ya dace.
Ya kuma gode wa gwamnan da gwamnatin jihar bisa damar da aka ba shi, tare da yi wa jihar Kano fatan cigaba da nasara a nan gaba.
Ganduje ya yi wa Abba maraba zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbi Gwamna Abba Kabir zuwa jam'iyyar.
Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, cewa zai yi nasara a zaben gwamna na shekarar 2027.
Hakazalika, ya ya bayyana dawowar Gwamna Abba zuwa APC a matsayin abin tarihi kuma mai alfanu ga jam’iyyar da kuma jihar Kano baki ɗaya.
Asali: Legit.ng


