Ta Faru Ta Kare: Gwamna Abba Ya Shiga Jam'iyyar APC a gaban Ganduje da Barau
- Bayan tsawon lokaci ana tirka-tirka a siyasar jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam''iyyar APC mai mulkin Najeriya a hukumance
- Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ne suka karbi Gwamna Abba yau Litinin
- Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan Abba ya mika takardar ficewa daga jam'iyyar NNPP a mazabarsa da ke karamar hukumar Gwale a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a hukumance a yau, Litinin, 26 ga watan Janairun 2026.
Gwamna Abba, wanda ake wa lakabi da Abba Gida-gida, ya sanar da hakan ne a wani gagarumin taro da aka shirya a babban dakin taron da ke gidan gwamnatin jihar Kano.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Gwamna Abba na shiga APC, Ganduje ya fadi jagoran jam'iyyar a Kano

Source: Facebook
Gwamna Abba ya koma APC a hukumance
Rahoton TVC News ya nuna cewa Gwamna Abba ya shiga APC ne a gaban tsohon shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. bdullahi Umar Ganduje.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila da Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi Ata da wasu manyan baki sun halarci taron.
Abba ya jaddada cewa dalilin komawarsa APC shi ne domin samar da kyakkyawar dangantaka da hadin kai tsakanin Kano da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jawabin Gwamna Abba a taron shiga APC
Gwamnan ya bayyana cewa burinsa na samar da hadin kai, kwanciyar hankali, da kuma hanzarta kawo ci gaba a fadin jihar ne ya ja shi zuwa APC.
"Idan Allah ya yarda (bayan komawarmu APC) zq ku ga canji, za ku ga karin ayyuka, za ku ga ci gaba, ba za mu zauna a cikin duhu mu zama makafi fa, lokaci ya yi da za su hada kai da gwamnatin tarayya.
"Za ku ga hadin kan da baku taba gani ba a Kano, za ku ga ayyukan ci gaba sosai," in ji Gwamna Abba.

Source: Facebook
Idan za a tuna, Abba ya fice daga jam’iyyar NNPP a ranar Juma’a, inda ya dora laifin ficewarsa kan tsananin rikicin cikin gida da kuma takaddamar shugabanci da ta dade tana addabar jam’iyyar.
A cewarsa, babban abin da ya sa a gaba shi ne samar da shugabanci na gari da kuma mika romon dimokuradiyya ga mazauna jihar Kano, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin wannanataki na Abba na iya sauya fasalin siyasar Kano da ma Arewa gaba ɗaya, yayin da ake sa ran APC za ta ƙara ƙarfi a jihar.
An kafa tutocin APC a gidan gwamnatin Kano
A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa an kawata fadar gwamnatin jihar Kano da sababbin tutocin jam'iyyar APC bayan cire na NNPP.
Bayanai sun nuna cewa tun daga kofar shiga gidan gwamnatin har zuwa cikin ofisoshi, duk an maye gurbin tutocin NNPP da na APC.
Gwamnatin Kano dai ta bayyana sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC a matsayin komawa gida kasancewar ya taba zama a jam'iyyar a shekarar 2014.
Asali: Legit.ng
