Ranar Cin Amana Ta Duniya: An Tona wa Kwankwaso Asiri bayan Abba Ya Bar NNPP

Ranar Cin Amana Ta Duniya: An Tona wa Kwankwaso Asiri bayan Abba Ya Bar NNPP

  • Dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Kano, Hon. Aliyu Sani Madaki, ya zargi Sanata Rabiu Kwankwaso da cin amana
  • Madaki ya mayar da martani ne kan furucin Kwankwaso da ya kira 23 ga Janairu 2026 a matsayin “Ranar Duniya ta Cin Amana”
  • Ya ce a ganinsa, 23 ga Fabrairu 2019 ce ta fi dacewa a kira ranar cin amana, saboda a wancan ranar Kwankwaso ya watsar da ‘yan takararsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Kano, Hon. Aliyu Sani Madaki, ya caccaki Rabi'u Musa Kwankwaso bayan korafi kan cin amana a siyasa.

Madaki ya taba jagoran tafiyar Kwankwasiyya ne kan kalamansa na ranar 23 ga Janairu 2026 a matsayin “Ranar Cin Amana ta Duniya.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya karbi shawarar wani bawan Allah kan ayyana ranar butulci ta duniya

An soki Kwankwaso kan zargin Abba da cin amana
Rabiu Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Madaki ya yi wannan martani ne a shafinsa na Facebook inda ya ce ai babu mafi cin amana a siyasa kamar yadda Rabi'u Kwankwaso ya yi wa Atiku Abubakar a shekarar 2019.

Zargin cin amana da Kwankwaso ya yiwa Abba

Kwankwaso ya yi wannan furuci ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road a Kano.

Sanata Kwankwaso ya fadi haka ne bayan sanarwar murabus ɗin Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP wanda ake hasashen zai koma APC.

Jagoran Kwankwasiyya ya ce ya aminta da wannan lamari ne bayan ya ga wani ya bukaci sanya ranar a kafofin sadarwa wanda ya ce ya dauki hankalinsa sosai.

Hon. Madaki ya mayar da martani ga Kwankwaso

Amma Madaki, wanda ya fice daga NNPP tun Nuwamba 2024, ya ce Kwankwaso shi ne babban mai cin amana, yana mai cewa a 23/02/2019 ya watsar da ‘yan takararsa tare da cin amanar Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Kwamishina ya dauki layinsa tsakanin Abba Kabir da Kwankwaso

Da yake mayar da martani a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook cikin harshen Hausa, Madaki, mai wakiltar mazabar Dala a Majalisar Wakilai, ya ce:

Ni kuwa a gani na,ranar 23/02/2019 ita tafi dace da wannan suna na ranar butulci ta duniya."
Dan majalisar tarayya ya dura kan Kwankwaso kan cin amana
Dan majalisar tarayya, Hon. Ali Madaki da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Hon. Ali Sani Madaki, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Dan majalisa ta tuna rashin mutuncin Kwankwaso

Madaki ya ce ranar da Kwankwaso ya yi watsi da yan takara saboda wata yarjejeniya da jam'iyyar APC ita ce rana mafi cin amana da aka yi a siyasa.

Domin ranar 23/02/2019 ne Sanata Kwankwaso ya tsayar da yan takara kuma ya kayar dasu akan wani yarjejeniya da yayi da APC a lokacin sannan yaci amanar Atiku Abubakar, kuma kudin zabe da Wazirin Adamawa ya bayar aka ki rabawa sai bayan lokaci ya kure aka ba da kadan domin huce haushin faduwar Port Harcourt.

- Cewar Ali Madaki

Kwamishina a gwamnatin Abba ya yi murabus

A baya, mun ku labarin cewa kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Kano, Yusuf Ibrahim Kofarmata, ya yi murabus nan take a gwamnatin Abba Kabir.

Kofarmata ya ce yanayin siyasar yanzu na iya kawo shakku kan ‘yancin aikinsa da gaskiya, lamarin da bai dace da ka’idojin mukaminsa ba.

Ya gode wa gwamnatin Kano bisa damar aiki, yana fatan murabus dinsa zai taimaka wajen kare martabar ofishin da amincewar jama’ar jihar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.