Akwai Kura: Hannatu Musawa Ta Yi Gargadi kan Ajiye Kashim Shettima a 2027
- Ministar al'adu da yawon bude ido, Hannatu Musawa ta gargadi APC kan sauya tikitin Tinubu–Shettima kafin 2027
- Hannatu Musawa ta ce sauyin zai iya jawo asarar kuri’u a Arewacin Najeriya kuma akwai barazanar cewa ba za a kai labari ba
- Ta bayyana cewa siyasar Arewa tana da tsari da tunani na musamman, kuma dole a nazarce shi da kyau kafin yanke hukunci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministar al’adu da yawon bude Ido, Hannatu Musawa, ta shawarci jam’iyyar APC da ta yi taka-tsantsan dangane da takarar 2027.
Ta ce duk wani shiri na sauya tikitin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen 2027, na iya jawo wa jam’iyyar babbar matsala ta siyasar Arewa.

Source: Facebook
Musawa ta yi wannan jawabi ne a wata hira da aka yi da ita a shirin Mic On Show wanda ɗan jarida Seun Okinbaloye ke gabatarwa,da Theo Abu ya wallafa a X.
Hannatu ta yi gargaɗi kan zaben 2027
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a hirar, Hannatu Musawa ta yi maganganun da ke yawo a kan yiwuwar sake duba tsarin tikitin Musulmi da Musulmi da APC ta yi amfani da shi a zaɓen 2023.
A cewarta, cire Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ko sauya shi da wanda ba Musulmin Arewa ba zai haifar wa APC da ƙalubale musamman a manyan jihohin Arewa.
Ta bayyana cewa fahimtar yanayin tunanin al’umma a yankin na da matuƙar muhimmanci kafin ɗaukar irin waɗannan matakai.

Source: Facebook
A kalaman ta:
"Idan babu Bahaushe, Bafullatani ko Barkanuri Musulmi a kan wannan tikiti, to hakan na zama tangarda. Wannan shi ne gaskiyar yadda mutane ke tunani."
Hannatu ta magangantu kan zabe a Arewa
A cewar Hannatu Musawa, mutanen Arewa suna ɗaukar zaɓe da muhimmanci sosai, suna kallon kada ƙuri’a a matsayin wata hanya ta nuna tasirinsu a cikin tsarin mulki.
Ta ambaci jihohi kamar Katsina, Kano, Kaduna, Kebbi, Jigawa, Zamfara da Sokoto a matsayin wuraren da ake sa ido sosai kan duk wata shawarar siyasa.
Hannatu Musawa ta ce:
“Ainihin Arewa na fahimtar siyasa a mataki mai zurfi. Siyasa a can hanya ce ta rayuwa. Mutane kan jira duk bayan shekaru huɗu domin su fito su kaɗa ƙuri’a, domin a nan ne suke jin suna da tasiri."
Ta yi watsi da ra’ayin cewa APC za ta iya sauya tikitinta ba tare da fuskantar sakamakon zaɓe ba, tana mai cewa irin wannan tunani kuskure ne wajen fahimtar yanayin siyasar Arewa.
Dangane da jam’iyyun adawa gabanin 2027, Hannatu Musawa ta ce ba ta gamsu da cewa yan adawa da suka haɗu a jam'iyyar adawa da su iya kayar da APC ba.

Kara karanta wannan
2027: Atiku ya fara bambami tun yanzu, ya soki Sanatoci kan taba dokar zabe a majalisa
Rashin hoton Kashim ya hargitsa APC
A baya, kun ji cewa rikicin cikin gida a jam’iyyar APC a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na neman dawowa saboda kokarin nuna wariyar ga Kashim Shettima.
Rahotanni sun nuna cewa rashin sanya hoton Shettima a cikin babbar banar da aka rataya a wani taron APC a jihar Borno ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma fusata wasu mahalarta taron.
Babbar banar da aka yi amfani da ita a taron na ɗauke da hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin APC guda biyar na jihohin Arewa maso Gabas, amma ba Kashim.
Asali: Legit.ng

