Tsofaffin 'Yan Majalisa Sun Yi Watsi da Mara wa Tinubu Baya a Zaben 2027

Tsofaffin 'Yan Majalisa Sun Yi Watsi da Mara wa Tinubu Baya a Zaben 2027

  • Tsofaffin ‘yan majalisa 17 a Najeriya sun yi watsi da taron da ya amince da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ya yi wa’adi na biyu a kasar nan
  • 'Yan majalisar sun bayyana cewa an bi kudi ne kawai wajen shirya taron, ba wai tuntuba ta gaskiya a kan batun zabe mai zuwa ko makomar kasa ba
  • Sun bukaci a auna mulki da aiki, ba da shaidar goyon baya ba kawai za a rika goyon bayan Bola Tinubu ya zarce a karagar mulki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tosfaffin 'yan majalisar tarayya 17 sun nesanta kansu daga wani taron takwarorinsu da aka kira domin amincewa kan zaben 2027.

Wasu daga cikin tsofaffin 'yan majalisa sun yi taron domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya na neman wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Hannatu Musawa ta yi gargadi kan ajiye Kashim Shettima a 2027

Tsofaffin yan majalisa sun barranta kansu da goyon bayan Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar tsofaffin 'yan (NFFL) ne suka bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu a ranar Asabar, 24 ga watan Janairu, 2026.

Yadda aka yi taron goyon bayan Tinubu

Jaridar Thisday ta wallafa cewa Shugaban ma'aikatan fadar Shugaban Kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ne ya kira taron.

Taron ya hada tsofaffin ‘yan majalisa daga bangarorin siyasa daban-daban. Daga cikinsu akwai tsofaffin Shugabannin Majalisar Dattawa Pius Anyim.

Sauran sun hada da Ken Nnamani, da tsofaffin Kakakin Majalisar Wakilai Patricia Eteh da Yakubu Dogara, da sauransu.

Sai dai wata kungiya ta tsofaffin ‘yan majalisa ta mayar da martani, tana bayyana cewa ba ta da alaka da duk wani taro da aka shirya da sunan dandalin tsofaffin ‘yan majalisa.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar a ranar Asabar, sun gargadi jama’a kada a ruɗe su da abin da suka kira “aikin siyasa da aka shirya a fili.

Kara karanta wannan

APC ta shirya, an ji muhimman dabaru 4 da za su iya sa Tinubu ya lashe zaben 2027

Matsayar tsofaffin yan majalisa kan Tinubu

Tsofaffin 'yan majalisa sun kara bayyana cewa ba za su taba shiga irin wannan taro da aka haka domin nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu ya zarce ba.

Tsofaffin yan majalisa sun kalubalanci gwamnatin Tinubu kan neman takara
Shugaban kasa Tinubu a gaban yan majalisa a zaman hadin gwiwa Hoto:Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewarsu, an shirya wannan taro ne domin a nema wa Shugaba Tinubu goyon bayan tsofaffin 'yan majalisa saboda kudi ba wai mafitar kasa ba.

Sun bayyana taron a matsayin bikin siyasar kudi-da-kaya, inda aka tara wasu mutane kalilan domin kirkirar sahalewar karya.

Sun kuma yi gargadi da kar a yi amfani da sunayensu ko martabarsu ba tare da izini ba, suna cewa tsofaffin ‘yan majalisa ba kaya ba ne na cinikayyar siyasa.

Daga cikin masu sanya hannu a kan sanarwar akwai Hon. Sergius Oguns, Herman Hembe da Sam Okwu, Zakari Mohammed.

Sauran sun hada da Tom Zakari, Mohammed Soba, Chika Adamu, Sadiq Ibrahim, Tajudeen Ajagbe da Supo Abiodun.

Sai kuma Danlad Donald Olayonu, Abubakar Amuda Kannike, Rufus Omiri, Mayor Eze, Kamil Akinlabi, Shaaba Ibrahim, da Nkwo Nkole.

Kara karanta wannan

2027: Alamu sun nuna wasu ministoci da hadimai za su rasa mukamansu a gwamnatin APC

Tinubu ya yi magana game da mulkin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bayani kan halin da yake ciki dangane da tafiyar da mulkin Najeriya, inda ya bayyana cewa akwai nauyi matuka.

Shugaba Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026, a yayin da yake neman afuwa bisa jinkirin rantsar da sabon kwamitin gudanarwa na Hukumar FCC.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa kula da al’amuran Najeriya ba ƙaramin aiki ba ne, yana mai jaddada cewa akwai manyan nauye-nauye da ke kan gwamnati a lokaci guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng