Abin da Abba Ya Fadawa Kanawa yayin Raba Babura 600 bayan Ficewa daga NNPP

Abin da Abba Ya Fadawa Kanawa yayin Raba Babura 600 bayan Ficewa daga NNPP

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargadi masu amfani da kafafen sada zumunta su rika kirkirar abubuwa cikin ladabi
  • Ya bukace su da su yi amfani da kafafen sada zumunta wajen karfafa hadin kai, ci gaba da wayar da kan al’umma
  • Gwamnan ya bayyana shirin tallafa wa masu a matsayin hanya ta karfafa matasa da rage talauci a Kano yayin raba babura

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano – Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta su gudanar da aiki a tsanake.

Abba ya yi kiran ne musamman magoya bayan gwamnatinsa, da su tabbatar suna kirkirar abubuwa masu kyau, girmamawa da mutunci domin karfafa hadin kai da ci gaba.

Abba ya gwangwaje matasa da babura 600 a Kano
Jerin babura 600 da Abba Kabir ya rabawa matasa a Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Facebook

Abba ya raba babura 600 ga matasa

Kara karanta wannan

Kasuwar teloli da ƴan yadI ta bude suna caɓawa ana shirin karbar Abba a APC

Wannan kira na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan ya yi wannan kira ne a yayin wani shirin rabon babura na tallafa wa masu amfani da kafafen sada zumunta daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

An ruwaito gwamnan yana cewa:

“Ina kira gare ku da ku rika yin abubuwa cikin ladabi, girmamawa da mutunci a yayin kirkirar abubuwan da kuke wallafawa. ‘Yancin fadin albarkacin baki dole ne ya kasance karkashin ka’idojin ɗabi’a, ladabi da girmama wasu.
“Mu yi amfani da kafafen sada zumunta a matsayin wata hanya ta hada kai, wayar da kan al’umma, ci gaba da kawo sauyi mai kyau, ba a matsayin wata hanya ta cin zarafi, kiyayya ko rarrabuwar kai ba. Ina kuma rokon ku da ku rika fifita Kano a duk abin da kuke wallafawa.”
Abba Kabir ya shawarci masu amfani da kafofin sadarwa
Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin taro a Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa.
Source: Facebook

Dalilin rabon babura 600 ga matasan Kano

Gwamna Abba ya bayyana cewa a wannan lokaci na fasahar zamani, kafafen sada zumunta sun zama wata babbar hanya ta yada labarai, fafutukar kare hakki, kirkira da kuma samar da hanyoyin samun kudin shiga.

Kara karanta wannan

Kujerar Hajji, sabon gida da wasu kyaututtuka 3 da Gwamna Abba ya yi waijin Fatima

Ya bayyana cewa an tsara shirin tallafa wa masu ne domin karfafa matasa, bunkasa tattalin arziki da tabbatar da dorewar ci gaba a fadin jihar Kano.

A cewarsa:

“Muna da yakinin cewa karfafa al’ummarmu, musamman mata da matasa, ita ce hanya mafi dacewa wajen rage talauci, rashin aikin yi da munanan dabi’u a cikin al’umma.”

Gwamnan ya kuma bukaci masu tasirin da su rika bayyana manufofin gwamnatinsa, musamman kudurin tabbatar da zaman lafiya da bunkasa tattalin arziki ta hanyar hadin gwiwa da sauran jihohi da kuma gwamnatin tarayya.

Kwankwaso ya ayyana ranar butulci ta duniya

Kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya amince da bukatar ware ranar 23 ga watan Janairun kowace shekara a matsayin ranar butulci ta duniya.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road a Kano yau.

Ya ce za su rika shirya bukukuwa da tarurruka a wannan rana domin tuna wa mambobin jam'iyyar abin da ya faru na butulci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.