Kwankwaso Ya Karbi Shawarar Wani Bawan Allah kan Ayyana Ranar Butulci ta Duniya

Kwankwaso Ya Karbi Shawarar Wani Bawan Allah kan Ayyana Ranar Butulci ta Duniya

  • Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya amince da bukatar ware ranar 23 ga watan Janairu a matsayin ranar butulci ta duniya
  • Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road a Kano yau Asabar
  • Ya ce za su rika shirya bukukuwa da tarurruka a wannan rana domin tuna wa mambobin jam'iyyar abin da ya faru na butulci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ayyana ranar 23 ga watan Janairu a matsayin “Ranar Butulci ta Duniya."

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ake sa ran yana kan hanyarsa ta komawa APC, ya sanar da ficewa daga jam’iyyar NNPP a ranar 23 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Kwamishina ya dauki layinsa tsakanin Abba Kabir da Kwankwaso

Kwankwaso.
Jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso yana magana da yan Kwankwasiyya a gidansa na Kano Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya ware ranar butulci

A wani bidiyo da hadiminsa, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya ce daga yanzu za su dauki ranar 23 ga kowane watan Janairu a matsayin ranar butulci.

Madugun Kwankwasiyya ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke hanyar Miller Road a Kano.

Kwankwaso ya yi ishara da wannan rana, inda ya bayyana cewa ra’ayin ayyana ranar ya samo asali ne daga wani mai amfani kafafen sada zumunta wanda ya nemi a ayyana wannan rana.

Yadda Kwankwaso ya amince da shawarar

Ya ce wannan shawara da ya gani a kafar sada zumunta ta matukar burge shi kuma ya amince da ita.

Tsohon gwamnan ya ce:

"Ina duba maganganun da ake yadawa a kafafen sada zumunta amma babu abin da ya fi daukar hankali na irin wanda ya wallafa cewa yana ba da shawarar mu ayyana ranar 23 ga Janairu ta kowace shekara a matsayin 'Ranar Butulci ta Duniya'.

Kara karanta wannan

Badaru ya gana da Kwankwaso bayan ficewar Abba daga NNPP? An gano gaskiya

"Saboda haka, a matsayina na shugaban wannan tafiya kuma jagora, ina sanar da cewa ina goyon bayan wannan shawara dari bisa dari. Daga yanzu za mu rika shiri a wannan rana don tunawa wadanda suka yi butulci."

Kwankwaso ya kara da cewa daga yanzu za a rika gudanar da bukukuwa na musamman a ranar domin tunatar da mambobin jam'iyyar abin da ya faru.

Yan Kwankwasiyya.
'Yan Kwankwasiyya a gidan Kwankwaso domin jaddada mubaya'a Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Dalilin ware ranar butulci ta duniya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Gwamna Abba ya bar NNPP a hukumance a ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida da takaddamar shugabanci ne suka tilasta masa daukar matakin.

Yayin da magoya bayan Abba ke murnar matakin a matsayin wani tsari na hikima don hadewa da gwamnatin tarayya, magoya bayan Kwankwaso kuwa sun bayyana shi a matsayin cin amana.

Yan Majalisa 22 sun bi Gwamna Abba

A baya, an ji cewa mambobin majalisar dokokin Kano 22 sun yanke shawarar bin tafiyar Gwamna Abba Kabir Yusuf a dambarwar da ke faruwa a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kakakin Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar ranar Asabar.

Sanarwar ta kara da cewa ‘yan majalisar sun amince da matakin gwamnan na barin NNPP, kuma suna jiran karin umarni kan mataki na gaba da za su dauka a siyasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262